United da Arsenal na son Kone, Williams na harin Arsenal

Manu Kone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manu Kone
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United ce kan gaba a zawarcin ɗan wasn Roma da Faransa Manu Kone, sai dai suna fusknatar hamayya daga Arsenal wajen siyen ɗan wasan. (L'Equipe - in French)

Arsenal sun sake matsa ƙaimi wajen ɗaukar ɗan wasan Athletic Club Nico Williams, da ke cikin tawagar Sipaniya da suka lashe gasa ci kofin duniya, anan kuma sa ran siyar da ɗan wasan kan fam miliyan saba'in da bakwai. (Teamtalk)

A karo na biyu West Ham ta ƙi amincewa da tayin da Roma ta yi wa ɗan wasanta na Crysencio Summerville, da fari dai an taya ɗan wasan kan euro miliyan 46 dai-dai da Fam miliyan 39. (Sky Sports Italia - in Italian)

Aston Villa na duba auna ko su siyar da Summerville saboda yadda suke neman wanda zai maye gurbin dan wasan Ingila Morgan Rogers, da ke shirin komawa Chelsea. (Talksport)

Barcelona sun shirya ganawa da Farren Torres, da ya ci wa Sipaniya ƙwallon da ta ba su damar cin gasar kofin duniya bayan doke Arjantina, domin jin menene shirinsa, kasancewar sauran shekara guda kwantaraginsa ya ƙare da Paris St-Germain. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Ipswich Town sun amince da ɗaukar dan wasan Morocco Isa Diop daga Fulham, kan euro miliyan 10, dai dai da fam miliyan 8.5. (Foot Mercato - in French)

Newcastle da Leeds na cikin ƙungiyoyin da ke buga gasar Firimiya da ke duba yiwuwar daukar dan wasan FC Midtjylland Franculino Dju, yayin da ƙungiyar ta Denmark ke neman fam miliyan 21 a msatyin farashin ɗan wasan dan ƙasar Guinea-Bissau. (Teamtalk)

AC Milan ta gano dan wasan Genk Konstantinos Karetsas, da zata ɗauka a kakar wasanni mai zuwa, sai dai za su iya siyar da dan wasn Portugal Rafael Leao, domin samar da kudin da za su yi hakan. (Gazzetta - in Italian)