Abin da ya sa ake shakku kan INEC gabanin zaɓen 2027

Joash Amupitan

Asalin hoton, INEC

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Ƴan siyasa da wasu ɗai-ɗaikun mutane a Najeriya na ci gaba da nuna shakku akan Hukumar Zaɓen kasar INEC wajen gudanar da sahihin zaɓe a 2027.

Mutum na baya da ya nuna irin wannan shakku shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, wanda ya buƙaci matasan ƙasar su tashi tsaye don kare dimokraɗiyya da kuma tabbatar da an gudanar da sahihin zabe a 2027.

Yayin wata hira da aka yi da shi wadda ta ja hankalin ƴan Najeriya, Mista Obi, ya ce ba bu tabbacin shugaban Hukumar Zaɓen ƙasar Joash Amupitan, zai gudanar da sahihin zaɓe, don haka dole ne ƴan ƙasar su tsaya tsayin daka don kwatarwa kansu ƴanci.

Kalaman na Peter Obi, da ya yi su a Jamus, sun fara jan hankalin ran 'ƴan Najeriya da dama.

Peter Obi ya bayar da misalai kan irin abubuwan da suka faru a ƙasar musamman irin abubuwan da jam'iyyun hamayya ke fuskata dama irin matakan da shugaban INEC din ke ɗauka wanda ya ce suna da ban tsoro.

Hussaini Ibrahim Abdulkarin, makusancin Peter Obi ne, ya shaida wa BBC cewa, dan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NDC, ya yi waɗannan kalamai ne saboda abubuwan da ke faruwa a Najeriyar baki ɗaya.

Ya ce," Ɗaukar ɓangaranci da ake yi a Najeriya shi ke sanya shakku a zukatan al'umar ƙasar inda ake gani kamare ba za ayi adalci a zaɓen 2027 ba."

Akwai dai jam'iyyun adawa da dama Najeriya da suma ke gani kamar akwai wani shiri na ƙarkashin ƙasa na haɗa kai tsakanin Hukumar INEC da kuma gwamnatin APC, don ganin cewa shugaba Tinubu ya samu damar lashe zaɓen da ke tafe.

Farfesa Abubakar Kari, ya shaida wa BBC cewa dole ne sai jam'iyyun hamayya sun haɗa ƙarfi da ƙarfe don ganin cewa sun kai ga gaci.

Ya ce,"Ba Peter Obi ne kaɗai ke yi wa hukumar INEC wannan zargi ba, akwai wasu jam'iyyun adawar da suma suka yi musaman jam'iyyar ADC, wadda ta yi zargin cewa kamar an kitsa wani abu ne na yin maguɗi a zaɓen da ke tafe."

" Bama jam'iyyun hamayya kaɗai ba, akwai wasu ƴan Najeriyar da masu sharhi da ke ganin cewa bisa la'akari da irin take-take da kuma kamun ludayin shugabannin hukumar ta INEC na wannan lokaci, ba sa kwantarwar masu zaɓe hankali akan cewa za ayi zaɓe na Allah da Annabi."In ji shi.

Duk ƙoƙarin da BBC ta yi don jin ta bakin hukumar IENC ɗin, akan wadannna zarge zarge da ake mata, abin ya ci tura.

Yadda jam'iyyun siyasa ke sukar INEC

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun bayan da hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana cewar Sanata David Mark ba shi ne shugaban jam'iyyar ADC ba, ta kuma cire sunansa daga shafinta da sauran jagorarin da suke ƙarkashinsa bisa dogaro da hukuncin kotu, 'yan jam'iyyar ta ADC ɓangaren Sanata David Mark suke ta caccakar shugaban hukumar.

A wani taron da suka gudanar a ranar 2 ga watan Afrilu, 'yan jam'iyyar ta ADC ɓangaren Sanata David Mark sun yi kira ga shugaban hukumar INEC ya yi gaggawar sauka daga muƙaminsa ko kuma gwamnati ta cire shi.

Taron wanda David Mark da sauran jagorrin jam'iyyar suka jagoranta ya ce yana fargabar ADC da sauran jam'iyyun adawar ƙasar ba za su samu adalci ba a zaɓen da za a yi a 2027 matuƙar Farfesa Amupitan ne ke shugabantar INEC.

"Ba mu yarda da shi ba, ba zai yi mana adalci ba, tamkar ɗan aiken gwamnati muke kallonsa, muna kiran da ya gaggauta murabus, ko kuma gwamnati ta sauke shi da kanta," in ji Sanata David Mark.

Ita ma babbar jam'iyyar adawa ta PDP ba a bar ta a baya ba wajen nuna rashin amincewa da jagorancin Amupitan.

Jam'iyyar ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki wanda ya yi wani taron haɗin gwiwa da jam'iyyar ADC, ya nuna shakkunsa bisa abin da ya kira rashin tabbas da kasancewa "dan amshin shata" ga jam'iyyar APC mai mulki da suka gani a tattare da Farfesa Amupitan.

Kabiru Turaki ya ce "muna tare da jam'iyyar ADC" a wannan gwagwarmaya ta neman adalci daga gwamnati ta hanyar "sauke Farfesa Amupitan daga shugabanci hukumar INEC" wadda ita ce za ta gudanar da zaɓe a 2027, saboda "imanin da muka yi cewa ɗan amshin shata ne".

Dole a cire Amupitan - SCSIAN

Cikin wata sanarwa da Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ƙarƙashin jagorancin Dr Bashir Umar ta fitar ta nuna takaicinta ga matsayar Gwamnatin Tarayya na ƙin sauraren ƙungiyoyin Musulmai na neman a sauke Farfesa Amupitan daga muƙaminsa.

SCSIAN ta ce yana daga cikin mutanen da suka "rubuta wasika ga Amurka" wadda ta kai ga ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da "ake kashe Kiristoci".

"Ya sayar da Najeriya a baya. Kuma zai sake sayar da ita a nan gaba. Duk wanda ya je yake gayyato 'yan mulkin mallaka zuwa lamarin da ya shafi cikin gidansa akwai buƙutar a yi masa wani kallo na musamman.

"Muna kaɗa ƙuri'ar yanke ƙauna ga Shugaban INEC. Gwamnatin Tarayya ya kamata ta maye gurbinsa da wani Kiristan da zai iya haƙurin zama da abokan zamansa Musulmai da sauran mabiya addinai".

Kuma sun bayyana damuwa dangane da yunƙurinsa na sabunta katin zaɓe da wani shiri na "hana Musulmai da dama samun damar kaɗa ƙuri'a" a zaɓen 2027.

Wane ne shugaban INEC?

An haifi Farfesa Amupitan ranar 25 ga watan Afrilun 1967 a garin Ayetoro Gbede da ke yankin ƙaramar hukumar Ijumu a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.

Ya yi karatunsa na furamare da sakandire a Kwara, sannan ya halarci Kwalejin Fasaha da ke Ilorin daga 1982 zuwa 1984, sannan ya zarce jami'ar Jos inda ya karanta fannin shari'a daga 1984 zuwa 1987, inda ya zama lauya a 1988.

Ya samu digirinsa na biyu a fannin shari'a a jami'ar Jos a shekarar 1993, sannan ya kammala digirinsa na uku a dai jami'ar a 2007.

Ya fara koyarwa a hukumar wallafa ta jihar Bauchi bayan kammala yi wa ƙasa hidima a shekarun 1988 zuwa 1989.

A yanzu haka shi ne mataimakin shugaban Jami'ar Jos, kuma shugaban hukumar gudanarwar jami'ar Joseph Ayo Babalola da ke jihar Osun.

A yanzu haka Farfesa ne a fannin shari'a a Jami'ar Jos da ke jihar Filato.

A shekarar 2014 ne ya samu babban muƙamin lauyoyi na SAN.