Hanyoyi 4 da mace za ta iya ɗaukar ciki waɗanda suka saɓa wa al'ada

Hoton mata masu juna biyu

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Ga duk mutumin da ya karanta darasin zamantakewa a makaranta wato social studies, zai iya sanin hanyoyin da ake samun haihuwa.

Yawancin mutane sun san cewa samun ciki na faruwa ne idan ƙwayar halittar namiji (maniyyi) ta haɗu da ƙwayar halittar mace (ƙwai) a lokacin da mace ke cikin kwanakin iya ɗaukar ciki.

Saduwa tsakanin mace da namiji ne hanyar da aka fi sani a matsayin hanyar samun ciki. Sai dai ba dukkan mata masu juna biyu ne suke samun cikin ta wannan hanya ba.

Akwai wasu hanyoyin da mace kan iya samun ciki da ba a saba gani ba, abin da wasu ke ganin tamkar ba zai yiwu ba.

1. Ta dubura

Duk da yake samun ciki ta hanyar saduwa ta dubura abu ne da yake da matuƙar wuya, masana sun ce hakan na iya faruwa. Amma irin hakan na faruwa ne kawai ga matan da ke da wata matsala ta musamman a tsarin haihuwa da ake kira 'cloacal malformation'.

Wannan matsala tana faruwa ne ga ɗaya cikin mata 50,000 da aka haifa, kuma galibi ana buƙatar sai an yi tiyata domin gyara ta.

Duk da haka, ko bayan an yi tiyatar, mai irin wannan matsalar na iya ci gaba da fuskantar wasu ƙalubale kamar na koda, rashin iya riƙe fitsari ko bayan gida, wahalar samun ciki, da haihuwar bakwaini.

.

Asalin hoton, Getty Images

A lokacin da jariri ke cikin mahaifa, akwai wata "hanya guda ɗaya" da ake kira cloaca, wadda daga baya take rabuwa ta zama mafitar fitsari, ta bayan gida da kuma farji.

Yana faruwa ga mutane, kamar yadda wasu dabbobi irin su tsuntsaye, ke da irin wannan hanya guda ɗaya wajen ɗaukar ciki.

A jikin maza a akwai wani nama da ya raba ramukan dubura zuwa biyu. Sai dai a wasu lokuta akan samu akasi bai raba tsakanin dubura da farji a jikin mace ba.

Maniyyin zai iya samun hanyar wucewa zuwa chemotaxis, wata hanya da ke kaiwa ga mahaifa wanda hakan ke da sauƙin haɗewa da ƙwayoyin halittar.

2. Ta baki

Yadda maniyyi ya wuce ta ciki iya isa zuwa ga ƙwan mace na daga cikin abin da ba a cika gani ba a tarihin likitanci.

Akwai matar da aka haife ta ba tare da farji ba, amma ta je wajen likita tana ƙorafin yadda take jin zafi a marar ta, kamar dai yadda ake naƙuda.

Bayan likitoci sun gudanar da bincike, sai suka gano cewa tana ɗauke da ciki, kuma ciwon da take ji alamar ta fara naƙuda ne.

Daga nan ne aka yi mata tiyatar haihuwa (CS), inda aka cire jaririn cikin nasara.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Maniyyi zai iya shiga cikin mace ya sadu da ƙwayoyin halittarta

3. Ba tare da saduwa ba

Akwai wata hanya da ake kira "splash pregnancy", wanda ke nufin samun ciki ba tare da an yi saduwar jima'i kai tsaye ba.

Wannan na iya faruwa ne idan aka fitar da maniyyi a kusa da wajen farjin mace, sannan maniyyin ya samu damar shiga cikin farji ya wuce zuwa ga ƙwayoyin halittar mace.

Kamar yadda bayanai suka nuna, idan maniyyi ya zube a kusa da farjin mace, akwai yiwuwar wasu daga cikin ƙwayoyin maniyyin su iya shiga cikin farjin, domin maniyyi na iya tafiya har zuwa inda yake neman ƙwan da zai haɗu da shi.

Sai dai ɗaukar ciki ta wannan hanya ba kasafai yake faruwa ba, saboda maniyyi ba ya wuce awa ɗaya a waje ba tare da ya lalace ba. Ko da yake a tsarin haihuwar mace, lafiyayyen maniyyi na iya tasiri har zuwa kwanaki biyar bayan ya shiga farji.

Maniyyi mai kyau na iya gudu cikin saurin da ya kai kusan milimita 5 a minti ɗaya.

.

Asalin hoton, Getty Images

Daga cikin ɗaruruwan miliyoyin maniyyin da ke shiga zuwa mahaifar mace a yayin saduwa, kusan ƙwayoyi 200 zuwa 300 ne kawai ke iya kaiwa ga ƙwan halittar mace.

Masana dai sun ce ba za a iya samun ciki ta hanyar shigar maniyyi a yayin wanka ba, domin ruwa yana rage tasirin maniyyin tare da rage danshin da ke taimaka masa ya rayu.

Haka kuma, sinadarai da ake samu a wasu ruwa, kamar chlorine, na iya kashe maniyyi cikin sauri, lamarin da ke hana shi iya zuwa ga ƙwayar halittar mace.

4. Samun ciki biyu lokaci ɗaya

Jikin mace yana da wasu hanyoyin kariya na halitta da ke hana samun wani sabon ciki yayin da take ɗauke da juna biyu.

Hakan ma yana faruwa ga matan da aka haife su da mahaifa biyu, domin waɗannan hanyoyin kariya suna ƙoƙarin hana faruwar wani sabon ciki na biyu.

A lokacin da mace take da ciki, sinadaran jikin dan'adam da ke hana jikin mace fitar da ƙwai daga mahaifa, sannan akwai wasu da ke rufe bakin mahaifa domin hana maniyyi wucewa zuwa cikin mahaifa.

Sai dai duk da haka wani yanayi da ake kira "superfetation" yana karya wannan tsarin kariya na jiki.

A wannan yanayin, mace kan iya fara ɗaukar wani sabon ciki na biyu bayan ciki na farko ya riga ya fara girma.

Ba kasafai aka fiye samun irin hakan ba, amma har masana ba su da cikakken bayani kan yadda hakan yake faruwa. Yawancin an fi samun hakan ga matan da aka taimaka musu ta hanyar sanya ƙwayoyin ɗaukar ciki

.

Asalin hoton, Getty Images

A mafi yawan lokuta, ciki na biyu na iya shiga kusa da kusa, da bambancin lokaci tsakanin mako biyu zuwa huɗu kacal. Wannan na nufin jariran biyu za su iya zuwa duniya a lokaci guda kamar tagwaye.

Duk da cewa akwai bambanci a shekarun cikin jariran, yawancin irin waɗannan cikin suna tafiya yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba.

Sai dai ba ko yaushe ake samun hakan ba, amma ba wani abin damuwa ba ne.

Amma idan mace ba ta shirin samun ciki a kurkusa, yana da kyau ta yi amfani da wata hanyar kariya domin kauce wa samun juna biyu ba tare da shiri ba.

Wannan bayani ya fito ne daga Farfesa Adam Taylor, darakta a Cibiyar Koyon Ilimin Halittar Jiki a Jami'ar Lancaster da ke Birtaniya.