Wasannin Hausawa na gargajiya da suka shuɗe da muhimmancinsu

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Wasannin al'adu na Hausawa na daga cikin muhimman abubuwan da suka bayyana salon rayuwa, halayya da kuma ɗabi'un al'ummar Hausawa tun fil azal.
Ba wai nishaɗi kawai waɗannan wasanni suke bayarwa ba, suna taka muhimmiyar rawa wajen koyar da tarbiyya da nuna jarumta da ƙara haɗin kai da haƙuri da dabarun rayuwa da ƙarfafa zumunci a tsakanin jama'a.
A al'adance, Hausawa sun kasance suna amfani da wasanni a matsayin wata hanya ta koyar da matasa rayuwa da shirya su domin fuskantar ƙalubalen zamantakewar rayuwa.
Wasu wasannin kuma na taimakawa wajen motsa jiki, wasu kuma suna haɓaka basira da tunani, yayin da wasu ke haɗa mutane tare a lokutan bukukuwa da tarurrukan al'umma.
Sai dai a wannan zamani, wasu daga cikin wasannin gargajiya na Hausawa sun fara raguwa sakamakon tasirin zamani da bunƙasar fasahar zamani da sauransu, wanda hakan ya sa wasannin da dama suka ɓace a yanzu.
BBC ta waiwayi baya domin tuna irin waɗannan wasannin tare da kuma ko suna da muhimmanci a yanzu.
Ma'anar wasannin gargajiya da muhimmancinsa
Dr Abu-Ubaida Sani, malami ne a sashen Harsuna da Al'adu da ke Jami'ar Tarayya
Gusau, da Dr Yakubu Aliyu Gobir na sashen Nazarin Harsunan Nijeriya a Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato sun haɗa hannu wajen rubuta littafin "Wasanni a ƙasar Hausa."
A cikin littafin, marubutan sun ce wasa dai na nau'in duk wata magana da aka furta ko wani aiki da aka aikata da nufin raha da nishaɗi. Yayin da aka ce wasannin dargajiya kuwa ana nufin wasannin Hausawa da suka kasance sanannu. Daga cikinsu akwai waɗanda suke da takamaimai wuri da lokacin aiwatarwa, wasu kuma har da sanannun kayan aiki da ake amfani da su yayin gudanar dawasannin.
Daga cikin wasannin gargajiya na Hausawa akwai na furuci wato waɗanda suka shafi magana. Sannan akwai wasannin kurma, wato waɗanda aikatawa ake yi ba tare da
wani furuci ba.
Littafin ya ƙara da cewa wasannin gargajiya sun kasance tamkar wata babbar
makaranta da Bahaushe ke amfani da ita wajen ilimantar da ƴaƴansa tare da koyar da su dabarun duniya da ma sauran ilimummuka da suka shafi rayuwa.
Daga cikin muhimmancin wasannin akwai:
- Motsa jiki
- Koyar da lissfi
- Ilimantarwa da taskace al'adu da kalmomin harshe
- Koyar da hikima da dabara
- Horo da gyaran hali
- Jarumta da bajinta
- Hannunka mai sanda
- Bin doka da ƙa'ida
- Nishaɗantarwa
- Hana yawon banza
- Sadar da zumunci
- Zurfafa tunani da wasa ƙwaƙwalwa da kaifafa basira
- Ƙarfafa danƙon zumunci
- Bayyana muradin zuci
- Wayewa da iya magana cikin jama'a
Wasan taɓaɓɓe

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasan taɓaɓɓe wasan tashe ne wanda yara maza ke gudanarwa cikin watan azumi. Yawan masu gudanarwar sukan kai misalin biyar ko sama da haka. Ɗaya daga cikinsu zai kasance jagora, wanda kuma shi ne taɓaɓɓe.
Ana gudanar da wannan wasa da dare, kamar dai sauran wasannin tashe. Amma wasu lokutan akan yi shi da hantsi ko da yamma.
Akan shiga gida-gida domin gudanar da wannan wasan tashe. Sannan sukan yi shi a dandali, wurin da taron jama'a suke. Kamar bakin shaguna ko wurin hutawa da
makamantansu.
Yadda ake yi shi ne ɗaya daga cikin yaran (Taɓaɓɓe) zai shafe fuskarsa da baƙin
tukunya ko gawayi ko dai wani abu makamancin wannan. Fuskar za ta zama gwanin ban tsoro. Daga nan zai nemi taɓarya ko sanda ya sa a kafaɗa. Sauran yara kuwa za su ɗaura masa igiya a ƙugu. Haka za su riƙa zuwa gida-gida yana kai wa jama'a bugu, tare da yi musu barazana da zazzare idanuwa. Sauran yara kuwa za su riƙa janyo shi
baya ta hanyar amfani da igiyar da suka ɗaura masa a ƙugu.
Waƙar Wasa
- Taɓaɓɓe: Ni ne baƙin birin nan da ake faɗi,
- Yara: Taɓaɓɓe!
- Taɓaɓɓe: Ba ga ni ba?
- Yara: Taɓaɓɓe!
- Taɓaɓɓe: A taɓa ni man!
- Yara: Taɓaɓɓe!
- Taɓaɓɓe: In rugurguza!
- Yara: Taɓaɓɓe!
Langa
Wani wasan da littafin ya ambato shi ne Langa, wanda yara maza suke gudanarwa yawanci tsakanin mutum biyar zuwa shida.
An fi gudanar da wannan wasa da dare, musamman lokacin da akwai farin wata mai haske, wanda ke haska dandalin da ake fi gudanar da wasan.
Yadda ake wasan shi ne yara sukan rabu zuwa ƙungiyoyi biyu. Wani lokaci kuma yakan kasance ɗaya daga cikin rukunnen ya ƙunshi yaran da suka zarce yawan ɗaya abokan karawar su. Hakan na faruwa ne yayin da aka tara masu iyawa ko manya.
Ana kiran kowane rukuni na lako. Daga nan ƴan garin ruwa za su tambayi
abokan karawar su; "Kun shirya?" Idan sun shirya za su amsa da:"Eh!" Daga nan ƴan garin ruwa za su ce: "Ruwa ta bayar." Da furta haka za a fara fafatawa.
Ƙwaƙwalati
Marubutan sun ce wasan ya zo ƙasar Hausa bayan cuɗanyar Bahaushe da baƙin al'ummu, musamman Turawa. Domin kuwa yara na kwaikwayon yadda ake ƙwallon ƙafa ne a cikin wasan.
Ana gudanar da wasan ne tsakanin yara biyu. Idan suka wuce haka, saura za su jira ne. Duk wanda aka cire, sai wani daban ya shiga gurbinsa.
Akan yi wannan wasa da hantsi ko da yamma ko da dare. Abin da ake buƙata kawai shi ne a samu wadataccen hasken da za a iya kallon ƴa wasa da kuma ƙwalluwa.
Akan yi amfani da gwangwanin mantileta ko na rof a matsayin gola, sannan ana tsara filin tamkar yadda filin wasa ƙwallon ƙafa yake, sannan kowane yaro yana da ƴanwasansa guda 11, ana bugawa da hannu.
Yaro zai ɗora faletinsa a gefen ɗan wasa ta sama, sannan ya ɗan danna da ƙarfi. Wannan ƙwanƙwlatin da ake bugawa shi zai je ya bugi ƙwalluwa, har a kai ga zuwa raga.
Wasu wasan
- Wasu fitattun wasannin yara masa sun haɗa da:
- A Sha RuwanTsuntsaye
- Jini Da Jini
- Belunge
- Allazi Wahidun
- Cincin Sakatum
- Balbela-balbela
- Damo Riya Damo
- Ɗanduƙununu
- Dokin Kara
- Danda Dokin Kara
- Mai ƙiriniya
- Tashi Mai Kwaɗayi
- Zule-Zuleyya
Ƴar Gala-Gala
Wannan wasa ne dangin bena. Saidai zubi da tsarinsa ya bambanta da na bena. Adadin masu gudanarwa na farawa daga biyu zuwa sama da haka.
Ana gudanar da wannan wasa ne a dandali, musamman da da hantsi ko da yamma yawanci a farkon damina.
Ana samun ƙaramin dutse ko fashasshiyar kwalba ko makamantansu a matsayin ƴar jifa. Sai a yi amfani da guntun kara ko ƙaramin itace a zana gidan dara manya a ƙasa. Gidajen akan yi su ne a jere da juna. Yawansu na iya kasancewa shida ko sama da haka.
Mai tafiya za ta jefa ƴar tafiyarta a gidan farko. Daga nan za ta fara tafiya tamkar dai yadda ake yi a bena. Da zarar an kammala gidaje gaba ɗaya, to za a yi talle. Wadda ta ci nasarar talle, to za ta sayi gida, cikin salon sayen gida a wasan bena.
Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana koyar da natsuwa.
Carafke
Wannan ma wasa ne da yara mata ke yi a cikin inuwa a dandali ko a da hantsi ko da yamma yawanci a ƙofar gida ko a cikin gida, kasancewarsa wasan zaune.
Yada ake yin shi ne masuwasa za su tsino duwatsu da ake kira ƴaƴa adadin da aka ƙayyade, misali goma-goma ko ashirin-ashirin ko makamancin haka. Daga nan za ta barbaza ƴaƴan wasa daidai son ranta. Sai ta riƙa jefa dodo sama sannan ta riƙa ɗaukar ƴaƴan da aka yi baje. Mai wasa za ta iya ɗaukar adadin ƴaƴan da ta ga dama a lokaci guda.
Yayin da mai wasa ta zo ɗauka, sai kuma ta girgiza, wato ɗaya daga cikin ƴaƴan da ke ƙasa ta yi rawa, to kuwa ta faɗi. Daga ƴarwasa ta gaba za ta karɓa.
Bayan an gama tsince duwatsun da aka yi baji da su, sai kowace 'yar wasa ta ƙirga waɗanda ke hannunta.
Yayin da aka gama cafke kowane baji, to wasa ta ƙare. Wadda tafi kowa yawan 'ya'ya za ta dali dukka sauran masu wasa. Daga nan kuma mai bi mata a maki ta dali saura.
Sakamakon carafke shi ne dala. Wadda za a dala za ta haɗa tafukan hannunta. Mai dala kuma za ta ɗauki takalmi ta riƙa dukan bayan hannun da shi.
Iye Nanaye
Wannan wasa ne na yara mata. Yara biyu ma na iya gudanar da wannan wasa. Sai dai yawansu na iya wuce haka.
Akan gudanar da wannan wasaa a dandali ko wurin biki ko wani wurin taron yara mata da hantsi ko da yamma ko da dare.
Yadda ake gudanar da wasan shi ne yara biyu za su fuskanci juna. Sannan za su fara waƙa tare da kuma tsalle. A duk lokacin da suka yi tsalle a tare, ɗaya za ta mai da ƙafafunta zuwa ɓarin dama ɗaya kuma ta mayar zuwa hagu.
Ga yadda waƙar take:
- Iye nanaye,
- Ayyaraye iye,
- Ayyaraye iye nanaye,
- Mu jekeFati,
- Ai Fati na gida,
- Ai Fati na gida,
- Ba ta zo ba.
- Ƙwaleru zai biya,
- Ƙwaleru zai biya,
- A ranar gobe,
- Ƙwaleru zai biya,
- Ƙwaleru zai biya wasanmu ragas.
Wasu wasa yara mata
- Digi-Digi
- Ɗan Balum-balum
- Kis-Kis-Kis An Kas-Kas-Kas
- Tafa-Tafa
- Jallu Wa Jallu
- Kwalba-Kwalba Dire
- Kande Mahaukaciya
- Ni Kura-Kura
- Ayye Rashidalle
- Carmama
Wasannin suna da tasiri a yanzu?
A game da a yanzu waɗannan suna da amfai, Dr Abu-Ubaida Sani ya ce har yanzu wasannin gargajiya suna da matuƙar muhimmanci.
"Duk da haka, an ce sarki goma, zamani goma. Idan kiɗa ya sauya, to rawa ma ya kamata ta sauya. A yanzu zamani ya zo da sababbin abubuwa da salon rayuwa ta musamman."
Ya ce daga cikin abubuwan da suka kawo canjin zamanin akwai:
- Tasirin karatun boko da na Islamiyya
- Tasirin shigowar talabijin
- Tasirin shigowar intanet da kafafen sada zumunta
- Tasirin wasannin cikin na'urori
- Sauyawan tsarin zaman Hausawa daga na cuɗe-ni-in-cuɗe-ka zuwa na ramin kura daga ke sai 'ya'yanki
- Tasirin gidaje na zamani da kange yara a cikin gida
- Tasirin ƙarancin amana a tsakanin mutane
- Tasirin kwaikwayon tsarin rayuwar baƙin al'ummu
Sai dai ya ce duk da haka, akwai damar zamanantar da wasannin tare da mayar da waɗanda suka dace cikin manhajoji.
"Wasanni da suke da nasaba da ƙwarewa a harshe da iya lissafi da sanin sunayen abubuwa (da makamantansu), duk ana iya mayar da su cikin manhajoji domin a rinƙa buga su a na'urori."
"Sauran wasanni da suke da alaƙa da motsa jiki kuwa, sai dai a zamanantar da su, sannan a riƙa gudanar da su a makarantu a lokacin fita tara ko kuma ranakun wasanni na makarantu. Wani abu mai muhimmanci kuma shi ne kundace wasannin domin ko da sun salwanta a zahiri, to ya kasance ana da su a rubuce na dindindin."










