Farashin mai na ci gaba da tashi a kasuwannin duniya

Asalin hoton, Getty Images
Farashin ɗanyen mai na ci gaba da ƙaruwa a kasuwannin duniya yayin da rikici ke ci gaba da ƙamari a Gabas ta Tsakiya.
A yau Talata, farashin mai ya ƙaru da kusan kashi biyu cikin ɗari, inda ya kai matakin da bai kai ba cikin makonni biyar.
Farashin ɗanyen man Brent ya haura kusan dala 92 kan kowace ganga, yayin da na West Texas Intermediate (WTI) ya haura dala 84 kan ganga.
Masana sun danganta hauhawar farashin da fargabar yiwuwar tangarɗa ga samar da makamashi daga Gabas ta Tsakiya sakamakon musayar hare-hare tsakanin Amurka da Iran, da kuma barazanar da mayakan Houthi na Yemen suka yi na ƙaƙaba katangar a hanyoyin jigilar mai zuwa Saudiyya.
Sai dai Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya (IEA) ta ce duk da cewa sabon rikicin ya ƙara jefa fargaba kan samar da makamashi, har yanzu kasuwar duniya na da ƙarfin da za ta iya jure wa wannan matsin lamba.
Shugaban hukumar, Fatih Birol, ya ce ƙara tsanantar rikicin da ya shafi mashigin Hormuz da cibiyoyin makamashi a yankin ya ƙara tayar da hankali kan samar da mai tare da haifar da rashin tabbas game da makomar kasuwar makamashi.































