Shugaban Uefa ya ƙauracewa wasan ƙarshe na Kofin Duniya don adawa da Fifa

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Turai Aleksander Ceferin bai halarci wasan ƙarshe ba na kofin duniya da aka yi tsakanin Spain da Argentina domin nuna adawa da Fifa.
Ka zalika bai je wasan farko na gasar ba da aka yi tsakanin Mexico da Afrika ta Kudu a Mexico City, maimakon haka ya wuce New Jersey ne abinsa a ranar Lahadi, kuma hakan na faruwa ne sakamakon wasu hukunce hukunce da Fifar ta yi wanda yake adawa da su.
Uefa ta nuna rashin jin daɗinta a fili bayan janye wa dan wasan gaban Amurka Folarin Balogun dakatarwar jankatin da aka ba shi saboda sa bakin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi.
Wannan na daya daga cikin abubuwan da suka harzuƙa shugaban Uefa ya ƙi zuwa kallon wasan ƙarshe.
Uefa ta soki matakin da Fifa inda ta bayyana shi da abin takaici da ba a yi zato ba wanda babu dalilin yin shi.





























