Me ya sa ƙasashen Turai suka fi mamaye Gasar Kofin Duniya ta 2026?

.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A tarihi, ƙungiyoyin Turai ba su cika taka rawar gani ba a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a wajen nahiyar.

Sau biyu kawai suka lashe irin wannan gasar tun shekara ta 1930 - Spain ta lashe gasar Afirka ta Kudu a 2010 sannan Jamus ta lashe gasar a Brazil shekaru huɗu bayan haka.

A shekarar 2026, ƙasashe shida daga cikin takwas da za su fafata a zagayen kwata fainal sun fito ne daga Turai, wato Belgium, Ingila, Faransa, Norway, Spain da Switzerland, yayin da Argentina da Morocco suma suka shiga jerin.

Wannan jeri shi ne mafi yawan ƙungiyoyin Turai da suka kai matakin daf da na kusa da ƙarshe a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a wajen Turai tun shekarar 1994.

Ƙarfin da ƙasashen Turai ke da shi a fagen ƙwallon ƙafa

Adadin ƙasashen Turai ya ƙaru yayin da gasar cin kofin duniya ke ci gaba, inda ƙungiyoyi bakwai daga cikin 10 na Turai su ka buga wasanninsu na farko na matakin rukuni ba tare da sun yi nasara ba.

Zafin Arewacin Amurka shi ne babban batun da aka fi tattaunawa kafin fara gasar yayin da ƙungiyoyi da dama, ciki har da Ingila, suka yi amfani da yanayi mai dumi don shirya wasanninsu na farko.

Bayan canjaras ɗin da Belgium ta yi da Masar, koci Rudi Garcia ya ce: "Ko digiri 10 ne ko digiri 30, dole ne mu ƙara ƙoƙari," yayin da kocin Switzerland Murat Yakin ya yi magana game da rashin kyawun aikin tawagarsa bayan kunnen doki 1-1 da Qatar, kuma bai ɗora alhaki kan yanayi ba.

Daga ƙarshe dai bayan kammala wasannin rukuni ƙasashen Turai sun yi nasara sau 17, sun yi canjaras sau 12 da rashin nasara sau bakwai a wasannin da suka buga da ƙasashen da ba na Turai ba .

"Wannan ya nuna cewa muna da tawagogin da za su iya lashe gasar cin kofin duniya," tsohon ɗan wasan gaban Ingila Wayne Rooney ya shaida wa BBC Sport bayan nasarar da Ingila ta samu kan Mexico.

A halin da ake ciki, Faransa ta yi fama da "dabaru masu tsauri" daga Paraguay don tsallakewa zuwa zagayen ƴan 16 yayin da Belgium ta fuskanci magoya bayan da ke buƙatar nasara a zagayen ƴan 16.

Belgium za ta fafata da zakarun Turai Spain a wasan daf da na kusa da na ƙarshe.

Me ya sa ƙasasehn Turai ke kan gaba?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai yiwuwar Turai ta sami wakilai da dama domin an ba ta damar tura tawagogi har 16 zuwa gasar cin kofin duniya - fiye da kowace nahiya.

Ƙasashen Turai kuma sun mamaye jadawalin FIFA na ƙasashen da suka fi hazaƙa a fagen ƙwallon ƙafa a duniya, inda biyar daga cikin manyan ƙungiyoyi takwas da ke saman kjadawallin suka kasance daga nahiyar. Portugal, wadda take matsayi na bakwai, Spain ta fitar da ita a zagaye na ƴan 16 na gasar cin kofin duniya.

Faransa ta fara gasar a matsayin wadda ake sa ran za ta lashe gasar cin kofin duniya, kuma tana taka rawar gani zuwa yanzu, inda ɗan wasan gaba Kylian Mbappe ke cikin waɗanda ke fafatawa a gasar don samun kyautar takalmin zinare (wanda ya fi kowa zura ƙwallaye) inda ya ci kwallaye takwas.

"Ba za a iya raina ƙarfin tawagar Faransa ba," in ji tsohon ɗan wasan tsakiyar Ingila, Danny Murphy, yayin da yake yin hasashensa kafin fara gasar cin kofin duniya.

"Ƴan wasa irin su Rayan Cherki da Ousmane Dembele da Desire Doue ba za su iya buga wasa a lokaci guda ba, amma suna iya sauya yanayin wasan idan suka shigo filin wasa, ko da kuwa bayan mintuna 70 sun shuɗe."

.

Tsohon mai tsaron baya na Faransa Gael Clichy ya ce: "Ina ganin Faransa, Spain da Ingila su ne ƙungiyoyi uku mafi ƙarfi".

Amma akwai ƙasashe da dama na Turai waɗanda suka yi wasa mafi kyau fiye da yadda mutane da yawa suka zata.

Norway tana amfani da dawowar ta zuwa gasar cin kofin duniya a karon farko tun 1998, inda Erling Haaland ya taimaka musu su wurin nuna kansu a matakin ƙasa da ƙasa.

Ɗan wasan gaban Manchester City ya zura ƙwallaye bakwai a gasar zuwa yanzu kuma akwai yiwuwar ya ƙara yawan ƙwallayensa a ranar Asabar.

A halin yanzu, Switzerland ta nuna ƙwarewa da natsuwa duk da fuskantar yanayi mai wahala a nasarar da ta samu a bugun fenariti a wasanta da Colombia a zagaye na ƴan 16.

Nasarar da suka samu na nufin tawagar Murat Yakin ta kai zagaye na takwas na ƙarshe na gasar cin kofin duniya a karon farko tun 1954, amma suna fuskantar ƙalubale inda za su fafata da mai riƙe da kambun gasar, Argentina.

Yakin ya ce, "Wannan lokaci ne na tarihi. "Mun kai matakin mafi kyau da tawagar Switzerland ta taɓa kai wa, amma tafiyar ta mu za ta ci gaba."

Tafiyar ta ci gaba yayin da ƙungiyoyin Turai ke ci gaba da fafutukar samar da ƙasar da za ta yi nasara a gasar cin kofin duniya ta 2026, musamman a gasar da ake bugawa a wajen nahiyar Turai.