Me ake yi da kadarorin da ake ƙwacewa daga waɗanda ake zargi da sata a Najeriya?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Majalisar Wakilan Najeriya ta bijiro da binciken yadda ake gudanar da kadarorin da gwamnati ke ƙwacewa daga hannun mutanen da ake zargi da rashawa a ƙasar.

A zamanta na ranar Talata, Majalisar ta bayyana damuwa game da yadda ake taskance kadarorin da ake ƙwatowar, ba tare da sahihan bayanan yadda ake adana su ba.

Majalisar ta ce akwai kadarori da dama da gwamnatin ƙasar ta ƙwato da suka haɗa da tsabar kuɗi da fikaye da motocin alfarma da gidaje da gine-gine da sauran kadarori tun bayan komawar ƙasar mulkin dimokraɗiyya.

Gwamnati kan ƙwato kadarorin ne bayan samun hukuncin kotu ta hanyar hukumomin ICPC da EFCC masu yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.

Ko a makon da ya gabata ma wata kotun tarayya ta bai wa EFCC damar ƙwace wasu kadarori fiye da 40 daga hannun tsohon ministan shari'ar ƙasar, Abubakar Malami da aka yi zargin ya mallake su ba bisa ƙa'ida ba.

Sai dai ƴanƙasar da dama na aza ayar tambaya kan yadda ake yi da kadarorin da ake ƙwatowar daga hannun waɗanda ake zargin.

Kan haka BBC tuntuɓi masana don jin yadda ake yi da kadarorin.

Mece ce ƙa'idar ƙwace kadarorin?

Akwai ƙa'idoji da hukumomi irin da ICPC da EFCC ke bi wajen ƙwace kadarorin mutanen da ake zargi da mallakarsu ba bisa ƙa'ida ba.

Muhammad Ashiru Baba tsohon daraktan wayar da kai da ilimantarwa na hukumar ICPC ya ce akan bi matakai daki-daki wajen ƙwace kadarorin.

Ya ce da farko idan hukuma ta samu ƙorafin cewa ga wani mutum ya mallaki kadarorin da suka zarta albashinsa ko samunsa idan ba ma'aikacin gwamnati ba ne, to za ta ƙaddamar da bincike.

''Za a ƙaddamar da binciken ne ba tare da sanin mutumin ba, idan hukuma ta kammala tattara bayanan da take bukata, sai ta kira shi domin ya kare kansa'', in ji shi.

Tsohon daraktan na hukumar ICPC ya ce idan mutumin ya gamsar da hukumar cewa wataƙila ya mallaka ne ta hanyar gado ko wata hanya halastaciyya daban da aikinsa shikenan sai a sallame shi.

''Amma idan ya kasa gamsar da hukuma kan hanyar da ya bi ya mallake su, to hukumar z ata tafi kotu, domin samun izinin ƙwace kadarorin amma na wucin gadi'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa bayan hukumar ta ƙwace kadarorin na wucin gadi, za a bai wa mutumin wani lokaci domin ya je kotu ya kare kansa, ma'ana ya gamsar da ita cewa ya mallaki kadarorin ne ta halastacciyar hanya.

Idan lokacin da doka ta ware masa na kare kansa a kotu - bayan ƙwace kadarorin na wucin gadi - ya ƙare bai iya gamsar da hukumar ba.

Hukumar ICPC ko EFCC za ta koma kotu domin ta samu izinin ƙwace kadarorin na dindindin, shikenan sun bar hannunsa.

Wane ne ke riƙe kadarorin?

Muhammad Ashiru Baba ya ce bayan kammala ɗaukar ƙwace dukiyoyin na dindindin, hukumar da ta ƙwace, wato ICPC ko EFCC za su ci gaba da kula da kadarorin, ƙarƙashin dokar kula da kadarori ta 'Assets Management Act'.

''Dokar ta ce idan kadara ce mai amfanar da al'umma kamar makaranta, za a ci gaba da amfani da ita, ba za a bari ta lalace ba'', in ji shi.

Haka ma ya ce idan gidan haya ne, masu hayar za su ci gaba da zama a gidan har zuwa wani lokaci.

Ya ci gaba da cewa idan makaranta ce hurumin karɓar kudin makarantar ya koma hannun hukumar da ta ƙwace kadarorin ba mutumin da aka ƙwace kadarorin daga hannunsa ba.

''Haka za a riƙa yi har tsawon wata uku ko shida, lokacin da doka ta ware wa mutumin ya kare kansa'', in ji shi.

Idan kuma an ƙwace su na dindindin to hukumar za ta rubuta wa gwamnati cewa da kadarori kaza ta ƙwato daga hannun mutanen da kotu ta samu da laifi.

Yaya ake yi da su?

Tsohon ma'aikacin na ICPC ya ce daga ƙarshen gwanjon kadarorin ake yi domin sayar da su.

''Daga ƙarshe gwamnati z ata nemi shawarar waɗannan hukumomi kan yadda za a yi da kadarori, wanda kuma shawarar ba ta wuce gwanjonsu'', in ji shi.

Bayan kammala sayar da su za a tura kudin zuwa asusun gwamnati da ke Babban Bankin ƙasa na CBN.

Dangane da yadda ake yin gwanjon kayayyakin kuwa, tsohon daraktan na ICPC ya ce doka ta yi tanadin cewa za a buga labarin gwanjon kadarorin a manyan jaridun ƙasar da kuma shafukan intanet na hukumomin domin sanar da mutane.

''Idan gida ne za a bai wa waɗanda suke cikinsa dama su fara tayawa, idan ba su buƙata ko suka gaza saya sai a bai wa na waje dama'', in ji shi.