Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da gaske gajimare ne ya faɗo a hanyar Abuja zuwa Kaduna?
A baya-bayan nan wani abin al'ajabi da ya ɓulla a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna wanda ya ɗauki hankalin matafiya da ke bin hanyar.
Abin mai kama da gajimare ya riƙa ɓulɓulowa daga ƙarƙashin ƙasa, inda yake taruwa ya riƙa tashi sama yana bazuwa a gefe.
Tun a makon da ya gabata ne abun ya fara ɗaukar hankalin matafiya, waɗanda suke sauka daga ababen hawansu tare da shiga cikinsa domin ɗaukar hotuna.
Mutanen da dama dai kan ce gajimare ne ya faɗo a wurin, wani ala'amari da ba a saba gani ba.
Shin gajimaren ne?
Hukumar Kula da Ka'idojin Muhalli ta Najeriya, NESREA, ta ce ta fara bincike domin gano musabbabin ala'amarin.
A ranar Talata ne tawagar jami'an hukumar suka ziyarci wurin da ke kusa da garin Jere a jihar Kaduna domin gane wa idansu.
Cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yaɗa labarai na hukumar, Nwamaka Ejiofor, ta fitar, ta ce jami'an NESREA sun ziyarci wurin domin gudanar da bincike.
Ta kuma ce daga binciken farko da suka gudanar sun gano cewa kumfa ce ke taruwa a wurin ba gajimare ba kamar yadda wasu ke yaɗawa.
Binciken farko da hukumar NESREA ta yi ya nuna cewa wata babbar mota ce ɗauke da wasu sinadarai ta yi hatsari a kusa da wurin, wanda ya janyo zubewar sinadaran da take ɗauke da su.
An gargaɗi masu taɓa kumfar
Kodayake hukumar ba ta tabbatar da ainihin abin da ya haifar da tashin kumfar ba, amma ta ce tana kan bincike domin gano haƙiƙanin abin.
NESREA ta ce ta tattara bayanai daga jami'an gwamnati da mazauna yankin, sannan ta ɗauki samfurin kumfar da ƙasar wurin da kuma ruwan wani rafi da ke kusa domin faɗaɗa bincike.
Hukumar ta kuma gargaɗi jama'a su guji kusantar kumfar da ruwan da ke kusa da wurin da kuma ƙasar da ke kewaye da shi har sai an kammala binciken, domin kauce wa yiwuwar haɗuwa da wani abu mai illa ga lafiya.