Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda tsawa ta kashe yara 6 ƴan gida ɗaya a Adamawa
Aƙalla yara shida ne tsawa sakamakon ruwan sama ta kashe tare da jikkata guda biyu, a lokacin da suke aikin roron gyaɗa a gona a jihar Adamawa.
Tsawa ko aradu dai na faruwa ne a lokacin da giragizai suka hau sararin samaniya dab da saukar ruwan sama ko kuma lokacin da ruwan ke sauka.
Ana yawan samun yanayin da tsawa ke kisa ko kuma jikkata mutane a lokacin damuna irin wannan.
Hakan ya sa BBC ta tuntuɓi masana kan hanyoyin kariyar kai daga illar tsawa a lokacin damuna.
"Yadda tsawa ta kashe ƴaƴana 6"
Malam Musa Maude Wukari wanda shi ne mahaifin yaran sannan kuma mai unguwar Wukari da ke ƙaramar hukumar Ganye a jihar Adamawa ya bayyana wa yadda al'amarin ya faru.
"Abin da ya faru da ruwan sama ya fara sauka sai wata mata wadda take da ƙaramin yaro ta buɗe lema a kusa da wata bishiya. Su kuma yaran duk sai suka taru a ƙarƙashin lemar. To da tsawar ta faɗo shi ne ta yi musu haka," in mai unguwa.
Malam Musa ya ƙara da cewa sauran yaran guda huɗu da suka jikkata Allah ne kawai ya kare su.
"Daga cikin mutum hudu da suka jikkata, yaro ɗaya ya samu matsalaa idanunsa inda ta sauya masa launin ido sannan na biyun kuma ta taɓa masa ƙafa. Amma ita wannan mata da yaron nata babu abin da ya same su."
Hanyoyi 5 na kariya daga tsawa
A kwanakin baya, BBC ta tuntuɓi Farfesa Mohammad Alhaji, ƙwararre kan muhalli kuma malami a jami'ar Aliko Ɗangote da ke Wudil a Kano inda ya lissafa dabarun kiyaye kai daga tsawa kamar haka:
- Gujewa abubuwa masu maganaɗisu: Da zaran aka ji rugugin tsawar idan kana gindin bishiya ko kuma turken wutar lantarki ko kuma maganaɗisu na wayoyi abin da ya kamata ka fara yi shi ne ka yi maza-maza ka bar wurin.
- Neman wurin Ɓuya: Sai ka rufe kunnenka ka tafi wurin ɓuya kuma bisa son samu a shiga irin gidajen ƙasa na gargajiya su ne suke kare mutane daga tsawa saboda ba sa ɗauke da maganaɗisu.
- A guji shiga cikin mota ko manyan gine-gine da sunan neman mafaka.
- Idan aka ga tsawa ka da a tsaya a fili fetal ko kuma saman gini.
- Ka da a tsaya a tsaye - A zauna a haɗe ƙafafu a wuri ɗaya tare da saka hannaye a cikin gwiwoyi da rufe kunnuwa.
Yadda ake samun tsawa
Farfesa Mohammad Alhaji ya yi bayani kan abin da ke haddasa tsawa.
"Ita tsawar na faruwa ne saboda yanayin haɗuwar giragizan a sararin samaniya wanda kuma haɗuwar tasu na haifar da ƙwayoyin maganaɗisu mai alamar tarawa da kuma alamar ɗebewa, to duk lokacin da suka haɗu dole ka ga walƙiya kuma dole ka ga tsawa." In ji Farfesa Mohammed
Dangane kuma da yadda ake samun walƙiya wadda mafi yawanci ke yi wa tsawar rakiya, ƙwararren ya ce maganaɗisu ne na haske da ke fitowa daga giragizan da ake yi wa laƙabi da raƙumin ruwa da Hausa ko kuma 'Cumulonimbus' da Turanci.
"Su waɗannan gira-gizai na hauhawa ne sakamakon wannan haske da yake faruwa. Idan aka haska sai ta zama mai zafi wadda za ta buɗe ta kuma ƙara kaurarewa ta cika wajen abin da ya sa dole ne ta fashe. To lokacin da ta fashe shi ne za ta zo a matsayin walƙiya sannan kuma tsawa ta biyo baya."
"To idan aka yi wannan tsawa da walkiya kuma bisa rashin sa'a mutum yana kusa da inda turakun wutar lantarki suke ko kuma yana kusa da wata doguwar bishiya. To wannan hasken shi ne yake biyowa wannan bishiyar ko kuma doguwar sandar wutar lantarkin ta zo ta samu mutane wanda idan kwana ya kare ma sai a rasa rai," in Farfesa Mohammed Alhaji.