Yadda ƙudirin dokar haramta wa'azi da talla a motocin haya ke tayar da ƙura a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Wata sabuwar taƙaddama ta taso sakamakon amincewar da majalisar dattawan Najeriya ta yi wa ƙudirin dokar nan da ya haramta gudanar da wa'azi da tallace-tallace a cikin motocin haya a ƙasar, wadda hukumar kiyaye hadura ta ƙasa, wato ''Federal Road Safety Corps'' ta gabatar.

Idan dai ƙudurin ya zama doka za a iya zartar da hukuncin tarar kuɗi naira dubu hamsin ko ɗaurin watanni shida a gidan yari ko kuma a haɗa duka biyun ga duk wanda ya karya ta.

Tun bayan da majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙudirin dokar batun ke ta jan hankalin jama'a inda suke bayyana mabambantan ra'ayoyi.

Tuni dai ƙungiyoyin addini da na kirista a Najeriyar suka bayyana matsayarsu kan wannan doka, inda ƙungiyar kare haƙƙokin musulmi a ƙasar MURIC, ta yaba da dokar.

Malam Sani Hassan Indabawa, shi ne shugaban reshen ƙungiyar ta Muric a jihar Kano, ya shaida wa BBC cewa, wannan ƙuduri da yanzu ake jiran sanya hannun shugaban ƙasa, abu ne mai kyau, kuma suna maraba da shi.

Ya ce,"Ƙuduri ne da Hukumar Kare Haɗurra ta Najeriya ta gabatar saboda ta lura da cewa da yawaitar afkuwar haɗura a kasar, saboda yadda masu wa'azi ke gabatar da wa'azinsu na ɗaukar hankalin direbobi abin da ke janyo haɗari har wani lokaci a rasa da dukiya."

" Maƙasudun dokar ke nan saboda yadda wa'azin ke jan hankalin direbobi, ba ma wa'azi kaɗai ba har ma da tallace tallace da kuma masu yin kasuwanci a cikin motar haya." In ji shi.

To sai a nata ɓangaren,majalisar kula da harkokin addinin kirista ta Najeriya, wato CCN, ta soki lamarin inda ta ce hakan wani mataki ne na tauye ƴancin gudanar da addini da walwalar jama'a, kuma za su ƙalubalanci dokar a kotu.

Rabaran Joseph John Hayab, shugaban reshen ƙungiyar kiristoci ta CAN a arewacin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, sam wannan doka ta saɓa doka.

Ya ce," A Najeriya akwai doka wadda ta nuna cewa kowa na ƴancin yin addininsa da ma tabbatar da shi, don haka ya za ace yin wa'azi a mota zai kawo haɗari, mu mun gane cewa mai makon a yi abin da zai taimaki al'umma, sai a kawo abin da zai tayar da hankali ya kuma ɓatawa mutane rai."

"Idan har aka sanya hannu a wannan doka, to za mu kai kotu." In ji shi.

Hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta Najeriya ta nemi a kafa dokar ne domin tabbatar da ana kiyaye dokokin hanya da rage afkuwar haɗurra.