Da gaske ne burodi na ɗauke da guba?

    • Marubuci, Badamasi Abdulkadir Mukhtar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wani abu da ake muhawara a kai game da kiwon lafiya, musamman a kafafen sada zumunta shi ne batun dacewar cin biredi ko ƙaurace mashi.

Wasu daga cikin likitoci sun riƙa fitowa su na gargaɗin mutane cewa biredi guba ne, inda suke gargadin mutane cewa su guji cin biredi, domin a cewar su yana da illa kuma yana janyo cututtuka musamman ga mutanen da shekarun su suka fara nisa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun masu fitowa su caccaki wani nau'in abinci cewa yana da illa ba.

To shin, mene ne illar burodi?

BBC ta tattauna da ƙwararren likitan cimaka, Dr Auwal Musa Umar, shugaban ƙungiyar masana ƙwararru a fannin cimakar abinci da alaƙar abinci da cututtuka na ƙasa reshen jihar Kano, inda ya yi bayanin matsayar wannan batu a ma'aunin masana.

Mene ne burodi?

Burodi ɗaya ne daga cikin abincin yau da kullum wanda al'umma suke amfani da shi wanda ake iya sarrafa shi daga garin alkama ko garin rogo ko kuma garin doya. ''Akan iya samo shi daga abin da a kimiyyance muke ce wa dangi na hatsi ko kuma na jiniya,'' in ji Dr Auwal.

Biredi ya kasu kashi biyu:

  • Mai laushi sosai, wanda ake yi da filawa. Shi ne ya fi yawa kuma mutane suka fi ci.
  • Mai dussa-dussa, wanda ake yi da alkama.

Burodi ya zamo abincin karin kumallo a mafi yawan gidaje, watakila saboda sauƙin sarrafawa da yake da shi. Akwai banbanci tsakani al'umma da kuma yankin da suka fito game da yadda suke haɗa nasu biredin da kuma yadda suke cin shi.

Wannan ya sa ake samun bayanai masu karo da juna a kan wannan nau'in abinci da ya yi fice. Amma masana cimaka irin su Dr Auwal Musa Umar sun yi bayanin matsayar biredi a ma'aunin kiwon lafiya da kimiyya kamar haka:

Da me ake haɗa burodi?

Masanin cimaka Dr Auwal Musa Umar na ganin cewa burodi wani nau'in abinci ne wanda sinadaran da aka haɗa shi ne za su iya tantance amfani ko rashin amfanin shi ga lafiyar ɗan Adam. Domin haka yana ganin ''ya danganta ga kamfanin da ke haɗa biredin ko kuma wane irin biredi ne da kuma sinadaran da aka zuba a ciki.''

Dr Auwal ya ƙara da cewa ana samun abubuwa kamar guda uku a cikin kayan haɗa biredi:

  • Garin fulawa (wanda shi ne jigo a haɗin biredi)
  • Mai ko kitse ko kuma 'butter'
  • Sinadarai da ake ƙarawa domin a samu abin da ake so na ɗanɗano ko kala ko ƙamshi ko kuma abin da zai sa ya daɗe ba tare da ya lalace ba.

Masanin cimakar ya ce a kimiyyance suna nazari ne a kan dukkan sinadaren da ke cikin abinci sannan su gano abin da yake ɗauke da shi na alfanu ko kuma na akasin hakan.

Ya ce a kimiyya ya kamata jikin mutum ya sami haɗin rukunnan abinci; mai bada kuzari da mai gina jiki da mai daidaita yanayin ɗumamar jiki da mai ba jiki kariya da mai inganta lafiya kuma mai taimakawa wajen narka abincin a jikin ɗan Adam.

''Dole sai jiki ya sami waɗannan sinadaran a lokaci guda kuma a kwano guda, shi ne jiki ya yi amfani da ingattaccen sinadaran da yake buƙata,'' in ji Dr Auwal. Ya ƙara da cewa ''to idan muka kalli biredi, ya mayar da hankali ne a kan muhimman sinadarai guda biyu; sinadarin kuzari (glucose) da kuma sinadarin maiko kitse waɗanda duk masu sanya kuzari ne kawai.''

Sinadarai masu illa a cikin burodi

Rukuni na uku na abubuwan da ake haɗa burodi da shi, wanda kuma masana ke ganin zai zamo ƙalubale ko matsala ga lafiyar ɗan'adam ya ƙumshi duk wani abu da aka ƙara shi a cikin abinci ana sane, saboda ya bayar da wani abu na daban daga ainufin aikin abinci.

''Mafi yawancin sinadarai da ake zuba wa shi burodin, gaskiya a nan ne Gizo ya ke saƙa kuma abin lura ga mutane,'' In ji Dr Auwal.

Masanin cimakar ya zayyano irin waɗannan sinadarai kamar haka:

  • Masu canza kalar biredi
  • Masu bashi damar daɗewa ba tare da ya lalace ba
  • Masu sanya ƙamshi
  • Masu sanya zaƙi/sikarin

Cutukan da biredi zai iya janyo wa

Dr Auwal Musa Umar ya ce ''biredin da aka fi amfani da shi a cikin al'umma a yau (mai laushi kenan) yana ɗauke da kamar kaso 75 zuwa kaso 85 na 'glacemic index' ma'ana kuzarin da jiki ya ke amfani da shi ko kuma yake buƙata a wannan rana.

''To a wannan gaɓar, wajibi ne al'umma su yi taka tsantsan da yawan cin biredi don wani bincike ma yana nuna cewa yawaitar cin biredi da jama'a ke yi, kuma ba su amfani da kuzarin yadda ya kamata, shi ya ke sanya jiki ya bijire wa sarrafa wannan kuzarin,'' in ji Dr Auwal.

Masanin ya ce yawan cin biredi a kullum, ba tare da mutum yana motsa jiki yadda ya kamata ba, ''akwai barazanar zai iya shiga yanayin da sinadaran da ke ciki za su iya haifar da wasu cutuka,''

Cutukan da Dr Auwal Musa Umar ya ce bincike ya tabbatar yawan cin biredi zai iya haifar wa su ne:

  • Ciwon daji ko kansa
  • Ciwon suga

Masanin ya ce wannan na faruwa ne saboda sinadaran da ake bai wa jikin sun zarce waɗanda yake buƙata, domin haka sai su sauya daga bayar da kuzari zuwa cutar da jikin.

Yadda ya kamata a ci biredi

Bincken da masana suka gudanar a matakai daban-daban sun tabbatar da cewa mutum zai iya cin biredi kuma ba tare da biredin ya cutar da shi ba, amma idan ya kiyaye wasu matakai ko sharuɗɗa.

Dr Auwal ya lissafa wasu daga cikin sharuɗɗan kamar haka:

  • Bayar da tazara: Mutum ya riƙa cin biredi a ƙalla sau 3 zuwa 4 a kowanne mako.
  • Motsa jiki bayan an ci biredi: Mutum ya kasance yana kwanciya ko yin bacci bayan cin biredi.
  • Kiyaye lokacin cin biredi: Mutum ya riƙa cin biredi a lokacin da zai fara harkokin yau da kullum ba lokacin da ya kammala hidimomi ba. Misali, ga masu zuwa aiki da safe, to a lokacin da gari ya waye ya dace su ci biredi, ba lokacin da suka tashi daga aiki ba.
  • Haɗa biredi da wasu abubuwa: Mutum ya riƙa cin biredi a haɗe da ganye kamar na kabeji, ko a haɗa shi da Tuffa ko wani ɗan itace marar zaƙi, ko kuma da dafaffen ƙwai. ''Kuskure ne cin biredi da soyayyen ƙwai saboda wannan man da aka soya ƙwai da shi zai haɗe da sinadaran cikin biredin ya zamo illa ga jiki,'' in ji Dr Auwal.
  • Kiyaye shekaru: Idan mutum ya yi nisan shekaru, ba biredi kawai ba, ana buƙatar ya ƙauracewa duk wani na'in abinci mai ƙara kuzari saboda a lokacin jikin nashi ba ya buƙatar su.

Likitan cimakan ya ce 'idan aka kiyaye yadda ya kamata a ci biredi, babu illar da zai yi wa lafiyar ɗan Adam, amma idan aka yi amfani da shi yadda bai kamata ba, biredi yana da babbar illa.