Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Gasar Kofin Duniya: Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai game da Gasar Kofin Duniya ta 2026 da aka kammala da sauran labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 20 zuwa 26 ga watan Yuli, 2026

An kammala Gasar Kofin duniya ta 2026 Spain ta lashe komai

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Martinez na shirin taka leda a Argentina

    Mai tsaron ragar Argentina Emi Martinez ya ce yana duba yiwuwar ko lokacin da zai hakura da buagawa ƙasarsa Argentina kwallo ya yi, bayan rashin nasarar da suka yi 1-0 a hannun Spain a wasan ƙarshe.

    Dan wasan mai shekara 33 ya yi nasara a wasanni 67 da ya bugawa ƙarsarsa kuma ya buga duka wasannin da suka yi guda takwas a gasar kofin duniya ba tare da an sauya shi ba ko sau ɗaya, kuma kwallo takwas kawai aka ci shi.

    Shi ne ya lashe kofin duniya a 2022, ya lashe kyautar golan da ya fi kowanne a gasar, kuma ya taka rawar a zo a gani a cikin gasar baki daya.

    Shi ne golan Aston Villa tun 2020, kuma kwantaraginsa zai ƙare ne a 2029, ko da yake ana alaƙanta shi da tafiya Juventus a wannan kakar.

  2. Lokacin saukar shugaban Fifa ya yi - in ji shugaban La Liga

    Shugaban gasar La Liga ta Spain Javier Tebas ya yi kira ga shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino ya sauka daga muƙamunsa.

    Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da wani gidan jari na La Gazzetta da ke Italiya, yana cewa Infantinno ' na neman lalata hukumar Fifa'.

    Ya kuma soki yadda ake hutun shan ruwa ana tsaka da wasa a yayin gasar, da kuma wani hutu na gaira babu dalili da aka je a wasan ƙarshe lokacin da aka kammala hutun mintina 45 na farko, ka zalika ya yi batun janye jan katin da aka yi wa dan wasan Amurka Folarin Balogun da kuma shirin mayar da gasar kofin duniya ta ƙasashe 64.

    Lokacin da aka tambaye shi ya kamata Infantino ya ajiye aiki sai ya ce " a ra'ayina eh, ya kamata, ina ganin lokacinsa ya yi."

  3. Fifa ta fara bincike kan kan faɗan da aka yi bayan wasan karshe

    Hukumar kwallon ƙafa ta duniya Fifa za ta fara bincike kan mummunar halayyar ta 'yan wasan Argentina suka nuna bayan kammala wasan ƙarshe na Kofin Duniya.

    Fifa ta nemi kwamitin ladabtarwarta ya samar da wani kwamiti da zai bincike kan lamarin domin tabbatar da abin da ya faru a filin wasa na MetLife.

    Duk ɗan wasa ko koci da aka samu da hannu cikin lamarin za a dakatar da shi, kuma za a ci tarar hukumar kwallon ƙafa ta Argentina.

    Bayan rashin nasarar da ta yi a hanun Spain 1-0 a ranar Lahadi, wasu 'yan wasa da kuma mutanen tawagar kocin Argentina sun kama rikici da yan wasan Spain lokacin da suke murnar cin wasansu.

    Nahuel Molina da Leandro Parades da Thiago Almada da mataimakin kocin Roberto Ayalla duka an gansu cikin rikicin.

  4. Shugaban Uefa ya ƙauracewa wasan ƙarshe na Kofin Duniya don adawa da Fifa

    Shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Turai Aleksander Ceferin bai halarci wasan ƙarshe ba na kofin duniya da aka yi tsakanin Spain da Argentina domin nuna adawa da Fifa.

    Ka zalika bai je wasan farko na gasar ba da aka yi tsakanin Mexico da Afrika ta Kudu a Mexico City, maimakon haka ya wuce New Jersey ne abinsa a ranar Lahadi, kuma hakan na faruwa ne sakamakon wasu hukunce hukunce da Fifar ta yi wanda yake adawa da su.

    Uefa ta nuna rashin jin daɗinta a fili bayan janye wa dan wasan gaban Amurka Folarin Balogun dakatarwar jankatin da aka ba shi saboda sa bakin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi.

    Wannan na daya daga cikin abubuwan da suka harzuƙa shugaban Uefa ya ƙi zuwa kallon wasan ƙarshe.

    Uefa ta soki matakin da Fifa inda ta bayyana shi da abin takaici da ba a yi zato ba wanda babu dalilin yin shi.

  5. Cin da aka yi mana akwai raɗaɗi in ji Messi

    Dan wasan gaban Argentina kuma kyaftin ɗin tawagar Lionel Messi ya ce "akwai raɗaɗi" a rashin nasarar da suka yi kuma "zai ɗauki lokaci mai tsawo kan ya warke", yana magana ne kan 1-0 da Spain ta ci su a wasan ƙarshe na Kofin Duniya da aka kammala.

    Dan wasan Spain na gaba Ferran Torres ne ya jefa kwallon a raga a lokacin da aka ƙara na minti 30 bayan cikar minti 90 da aka saba na wasa, wanda hakan ya kawo ƙarshen riƙe kofin da Argentina ke yi tun 2022.

    Har da wannan Messi ya yi rashin nasara biyu a wasan ƙarshe da ya taɓa zuwa, har da na 2014 a hannun Jamus.

    Dan shekara 39, da kamar wuaya ya halarci gasar ta 2030, ko da yake har yanzu bai bayyana ko zai hakura da bugawa ƙasarsa wasa ba.

    Messi ya fashe da kuka bayan tashi daga wasan lokacin da aka sa masa sarƙar da ake bayarwa ga wadanda suka buga wasan ƙarshe.

    "Ina taya Spain murna da lashe kofin nan da ta yi, ta zama gwarzuwar duniya", in ji Messi.

    An yi ta sukar Fifa bisa zargin cewa tana dauke kai kan Argentina a gasar da aka kammala, sai dai daga Fifa har Argentina babu wanda ya ce uffan kan zarge-zargen.

  6. Tsohon ɗan wasan Liverpool da Newcastle Keegan ya rasu

    Tsohon ɗan wasan Ingila kuma koci Kevin Keegan ya rasu yana da shekara 75.

    Rasuwar tasa na zuwa ne bayan sanar da kamuwa da ya yi da ciwon Kansa da ta kai mataki na huɗu.

    Daya daga cikin 'yan wasan Ingila da suka fi samun kyautuka a duniya, Keegan ya buga kwallo a Scunthorpe United, Liverpool, Hamburg, Southampton da kuma Newcastle lokacin da yake kan ganiyarsa.

    Daga baya ya zama kocin Newcastle da Fulham da Ingila da kuma Manchester City.

    A watan Yuni ne Keegan ya bayyana cewa yana fama da kansa a mataki na huɗu, wanda shi ne mataki mafi haɗari da ke nuna kansar ta bazu zuwa wasu sauran sassan jikinsa.

  7. Colossal Cubarsi

    Pau Cubarsí yana gaban duk wani dan wasa da ya halarci Kofin Duniya wajen:

    • Ya taɓa kwallo sau (139)
    • Ya ba da fassin ba tare da matsala ba sau (121)
    • Kashi (96%) na kwallo da ya ke bayarwa na zuwa daidai
    • Hana fassin kaiwa inda ake so (21)
    • Cire kwallo (6)
  8. 'Yan Spain na ci gaba da murna a Madrid

    Daren jiya tamkar rana ya kasance ga magoya bayan kwallon ƙafa a Spain.

    Ko mutum na kallon kwallo ko baya yi, dole yasa wani gagarumin lamari na faruwa a kasar.

    Haka aka wayi gari, kuma ana ci gaba da jiran tawagar ƙasar ta dawo daga Amurka.

    Wata murnarma sai sun iso.

  9. Spain ta isa gida

    Bayan kammala gasar Kofin Duniya babu abin da yake yin saura sai kuma kowa ya kama gabansa.

    Tawagar zakarun gasar Spain kamar kowa, ita ma ta nufi gida, kuma tuni ta isa.

    Ga dai yadda ta isa gida cikin hotuna.

    Kyaftin Rodri ɗauke da kofin duniyan a saman matattakalar jirgin, yayin da kocin tawagar Luis de la Fuente, ke tsaye a gefensa, suna dagawa masoya hannu.

    Wannan je motar da aka turo domin ta kwashi 'yan wasan Sifaniya da suka dawo daga gasar kofin duniya.

    Yan wasan Sifaniya na fitowa daga cikin jirgin, bayan kyaftin dinsu Rodri ya buɗe musu hanya.

    Duka 'yan wasan sun sakko daga jirgi suna jiran azo a ɗauke su.

  10. Duk da ya ci kwallo takwas amma bai ci kyauta ba

    Yadda gasar Kofin Duniya ta ƙare ga Messi ba abu ne mai dadi ba.

    Dan wasan mai shekara 39 ya fara gasar ne da cin kwallo uku rigis a wasan farko da suka buga da Algeria suka ci 3-0, inda ya yi kunnen doki da dan wasan Jamus Miroslav Klose da ke da kwallo 16 a gasar kofin duniya.

    Ya wuce nan har ya kai ga kafa tarihin wanda ya fi kowa cin kwallo a gasar kofin duniya ya kai kwallo 21.

    Amma damar ta kuɓuce masa ne bayan ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe ya ci kwallo biyu a wasansu da Ingila da suka yi 6-4, ya haɗa kwallo 10 a gasar ya kuma zama wanda ya fi cin kwallo a duka gasar ta maza da kwallaye 22.

    Wannan ne ya hana Messi kai wa ga lashe gasar.

  11. Messi bai samu dama ba

    A cikin minta 15 da fara wasa tsakanin Spain da Argentina, Lionel Messi sau daya ya iya samun damar taba kwallo tun da aka fara.

    Sau 54 kacal ya iya taba kwallo cikin mintina 120 da aka yi har da na ƙarin lokaci - kuma bai iya taɓa kwallo ba ko sau daya a cikin yadi na 18 na Spain a duka wasan.

  12. Abin da ya yi bai dace da kwallon kafa ba - Alan Shearer

    Tsohon dan wasan Ingila Alan Shearer ya yi martani kan abin da dan wasan Argentina [Leandro] Paredes ya yi bayan kammala wasan karshe na kofin duniya.

    "Shi ne ya je ya same su. Abin da ya yi baya cikin kwallon kafa.

    "Mun san muhimmancin kofin a wajensu, mun san zafin rashin nasara. Amma akwai yadda ake tafiyar da rashin nasara, in ji Alan.

    Ya ce an ta ganin Argentina suna irin wannan wasan na rashin girmama abokan wasansu.

    Ya ce abin da dan wasan ya yi bayan an tashi ba daidai ba ne.

    "Sun doke kasashe da dama a baya, saboda me su ba za a doke su ba". in ji dan wasan.

    We know how much it means to them and we know how much it hurts to lose, but there is a way to lose.

    Too many times we have seen that from Argentina.

    The reaction after the final whistle is terrible.

  13. Mbappe ya lashe kyautar wanda ya fi cin kwallo sau biyu a jere

    Kyauta ɗaya kacal da Spain ba ta mamaye ba ita ce ta wanda ya fi zira kwallaye a gasar.

    Dan wasan Faransa Khlian Mbappe ne ya lashe gasar karo na biyu kenan a jere.

    Dan wasan gaban ya ci kwallo 10 a wasa takwas da ya buga inda ya zarce Messi da lwaoo biyu.

    Ya ci kwallo takwas a gasar 2022 da aka yi a Qatar hakan ya sa a nan ma ya lashe irin kyautar a karo na farko.

    Dan Real Madrid din shi ne dan wasa na farko da ya fara cin kwallo 10 a gasa ɗaya a tarihi tun bayan dan wasan Jamus Gerd Muller a 1970.

    Magabacinsa a Faransa Fontaine da ya taba cin 13 a 1958, sai kuma na Hungary Sandro Kocsis da ya ci 11 a 1954, sune kawai suka taba cin kwallayen da ya fi na Mbappe a gasa ɗaya.

    Ya kuma zama wanda ya fi kowa cin kwallaye a tarihin gasar Kofin Duniya inda ya ci kallo 22 - yana saman Messi wanda ya ci kwallo 21, ya samu damar hakan ne bayan cin kwallo biyu a wasan neman na uku da suka yi da Ingila da aka tashi 6-4.

  14. Spain ta wawashe kyautukan Kofin Duniya

    Bayan mamayar da Spain ta yi a cikin filin wasa, mamayar ta ci gaba har zuwa bayan fage.

    'Yan wasan Spain sun cin ye kyautukan gasar, inda Kyaftin Rodri ya lashe dan wasan da ya fi kowa a gasar.

    Mai tsaron ragar tawagar da aka sa wa kwallo ɗaya kacal a gasar ya zama wanda ya fi kowa hazaka.

    Dan wasan bayan kasar And Pau Cubarsi mai shekara 19 ya zama dan baya mafi ƙoƙari a gasar.

  15. Yadda aka ga rana haka aka ga dare a Spain

    Ba a yi bacci ba a manyan biranen Sifaniya irinsu Madrid da Barcelona da dai sauransu.

    Yadda aka ga rana haka aka ga dare a biranen.

    Wata murna da suka kwashe shekaru 16 rabonsu da ita, kuma irinta ce ta biyu a tarihin kasar a Kofin Dunya.

  16. Matashiya kan wasan karshe na duniya

    Bayan wasanni 104 da aka buga cikin kwanaki 39 tsakanin ƙasashe 48, Spaniya ce ta lashe kofin bayan doke mai rike da kofin Argentina da ci 1-0.

    Dan wasan Barcelona Ferran Torres ne ya ci kwallon a mintina na 106 bayan Nico Williams ya dawo masa da ita a ka shi kuma ya maka ta cikin ragar kuma ta kwanta.

    Wannan nasara ce da kocin Spain Luis de la Fuente da ke rike da kofin Europe ya cancanci samu, bayan mamaye wasan da ya yi kan garzuwar Copa America.

    Argentina ta kammala wasan da mutum 10 bayan korar dan wasanta na tsakiya da ke wasa a Chelsea Enzo Fenendez, wanda ya samu katin gargaɗi guda biyu.

    Ferran Torres ya zama tamkar Iniesta da ya ci wa Spain kwallon da ta lashe Kofin Duniya da ita a 2010.

  17. Ta ɗaya a duniya

    Sifaniya ta yi murna da faranciki biyo bayan nasarar da ta samu ta lashe wannan kofi.

    Shugaban hukumar kwallon ƙafa ta duniya Fifa Giani Infantino da shugaban Amurka Donald Trump ne suka bai wa tawagar kofin.

    Ga yadda ta kasance cikin hotuna.

  18. Sifaniya za ta kwashi kudi masu yawa

    Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta bayar da sanarwar za a kara kudaden da ake baiwa dun tawagar da ta lashe kofin duniya tun kusan shekara guda baya.

    Fifa ta bayyana haka tare da kara yawan kasashen da za su halarci Gasar Kofin Duniya da aka kammala da suka kai 33.

    Yanzu Spain za ta karbi zunzuruntun kudi da suka kai dalar Amurka miliyan 51, mai makon miliyan 42.2 irin wanda Argentina ta karba a 2022 da ta lashe gasar.

    Argentina za ta karbi dala miliyan 43 kar a kan abin da ta karba lokacin da ta lashe gasar a baya.

    Ingila da ta zo matsayi na uku za ta karbi dala miliyan 30, daidai da abin da Spain ta karba a 2010 a matsayin gwarzuwar gasar.

  19. Barkanmu da rana

    Masu bibiyarmu barka da wannan lokaci kuna tare da Muhammad Buhari Fagge domin kawo muku labaran wasanni kai tsaye daga nan BBC.

    Za mu mayar da hankali ne kan abubuwan da suka shafi Kofin Duniya da aka kammala a jiya, wanda Sifaniya ta lashe, bayan doke Argentina 1-0.

    Sai ku kasance da mu.