Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda mutumin da bai yi suna ba a siyasa zai zama Firaiministan Birtaniya
- Marubuci, Rob Watson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, UK political correspondent
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Ba kasafai ba a shekarun baya-bayan nan wani ya zama Firaiminista ba tare da an yi masa cikakken bincike da tantancewa ba kamar Andy Burnham.
Saboda jam'iyyar Labour mai mulki ta yanke shawarar ba za ta gudanar da zaɓen shugabanci ba, sai dai za ta naɗa shi kai tsaye, ba a samu tattaunawa sosai kan manufofinsa ko salon mulkinsa ba.
Amfanin hakan shi ne an kauce wa rarrabuwar kawuna da ka iya cutar da jam'iyyar a bainar jama'a. Amma rashin amfanin kuwa shi ne sabon shugaba kuma firaiministanta bai samu gwaji da tantancewa sosai ba kafin ya hau mulki.
Ba da jimawa ba, za a ga irin Firaiministan da zai kasance. Amma yana da kyau a tuna cewa Burnham ba mutum ne da aka sani sosai ba – musamman a wajen yankin Greater Manchester, inda ya shafe shekaru goma yana matsayin magajin gari. Don haka kusan kowa zai kasance yana son sanin sa ne a hankali.
Abin da muka sani game da Burnham ya nuna yana da halayen mutum na waje da kuma na cikin tsarin siyasa. Kamar yawancin 'yan siyasa a yau, ya fi son jaddada bangaren da ke nuna shi a matsayin mutum na talakawa.
Ana kallonsa a matsayin mutum daga wajen masu iko saboda ya taso ne a cikin iyalin ma'aikata a arewacin Ingila. Amma kuma ana iya kallon sa a matsayin mutum daga cikin tsarin mulki saboda bayan ya kammala karatu a fitacciyar Jami'ar Cambridge, ya shiga siyasa da sauri, inda ya zama ɗaya daga cikin matasan haziƙan da suka yi fice a gwamnatocin New Labour na Tony Blair da Gordon Brown.
Dangane da halayyarsa, Burnham yana da ƙwazo wajen gabatar da kansa a matsayin mutum na kowa da kowa wanda talakawa za su iya danganta kansu da shi.
Yana son giya da kifi da soyayyen dankali, yana matuƙar son magana kan ƙwallon ƙafa da kiɗa, kuma kamanninsa sun fi na yawancin 'yan siyasar baya-bayan nan zamani da salo.
Game da siyasarsa kuwa, Burnham ya ce tun yana matashi ya ƙi manufofin Margaret Thatcher da gwamnatocin Conservative na shekarun 1980 waɗanda suka mayar da kamfanonin gwamnati zuwa ga masu zaman kansu tare da sassauta dokokin tattalin arziki.
Ya yi imanin cewa waɗannan manufofin ne suka sa masana'antu suka ragu tare da raunana tattalin arziki da ƙwarin gwiwar jama'ar Arewacin Ingila inda ya taso.
Yanzu ma, kamar yadda yake a lokacin, Burnham yana bayyana kansa a matsayin ɗan siyasa mai ra'ayin riƙau ba tare da jin kunya ba.
Kamar yawancin 'yan siyasar masu riƙau a Turai, Burnham yana kallon gwamnati a matsayin wata muhimmiyar kafa ta alheri, kuma ya fi mayar da hankali kan buƙatu da jin daɗin marasa galihu a cikin al'umma.
Sau da yawa yana sukar abin da yake kira tsarin tattalin arziƙi da ya fi bai wa ƴan kasuwa da masu zaman kansu dama shekaru 40 da suka gabata, wanda a cewarsa ya gaza biyan buƙatun talakawa.
Sai dai abin da yake nufi da wannan suka bai bayyana a sarari sosai ba, kuma bai taɓa nuna cewa yana da ra'ayin riƙau na siyasa ba ko kuma yana da sha'awa sosai kan cikakkun bayanai da ƙananan fannoni na manufofin gwamnati ba.
Shin Burnham zai kawo sauye-sauye masu girma a manufofin cikin gida ko na harkokin waje na Birtaniya?
Amsa a takaice ita ce: ba mu sani ba tukuna, domin tsokaci kaɗan ya yi kan waɗannan batutuwa.
Game da manufofin cikin gida, akwai manyan ƙalubale da suka takaita abin da zai iya yi.
Birtaniya na fama da ƙarancin bunƙasar tattalin arziƙi da kuma yawan bashin gwamnati.
Haka kuma, kashe kuɗaɗen gwamnati da haraji sun riga sun kai matakan da ba a saba gani ba a tarihin ƙasar.
Don haka, duk da cewa masu ra'ayin riƙau a cikin jam'iyyar Labour za su so gwamnati ta ƙara tsoma baki a tattalin arziki da ayyukan jama'a, hakan ba zai kasance mai sauƙi ba.
Har ila yau, gwamnatin Burnham za ta kasance ƙarƙashin takura saboda alkawarin da jam'iyyar ta yi a zaɓen da ya gabata na cewa ba za ta ƙara yawancin haraji ba, kuma ba za ta yawaita karɓar bashi domin ƙara kashe kuɗi ba tare da ƙa'ida ba.
Babban ra'ayin da Burnham ya fi bayyanawa tun bayan da aka zaɓe shi a matsayin shugaban jam'iyyar Labour mai jiran gado shi ne ƙara bai wa yankuna ikon cin gashin kansu , wato miƙa wasu nau'in iko da kuɗaɗe daga gwamnatin tsakiya da ke Landan zuwa yankuna daban-daban na ƙasar.
Sai dai har yanzu yadda zai aiwatar da wannan ra'ayi bai fito fili sosai ba, kuma bayanansa a kai suna da ƴar sarƙaƙiya.
A fannin manufofin harkokin waje – wani batu da Burnham bai cika magana a kai ba a tsawon rayuwarsa ta siyasa – ana sa ran za a ga ci gaba da manufofin da ake da su fiye da manyan sauye-sauye.
Kasancewar manufofin harkokin waje suna kasancewa ne sakamakon yanayin ƙasa, tarihi, muradun ƙasa da kuma abubuwan da ke faruwa a duniya, maimakon siyasar jam'iyya ko ra'ayin shugaban da ke mulki, irin wannan ci gaba da manufofi ba abin mamaki ba ne.
Saboda haka, kamar Sir Keir Starmer, Burnham zai yi ƙoƙarin ƙulla dangantaka mai ƙarfi da Tarayyar Turai (EU), amma ba har ta kai ga kusanci fiye da kima ba. Haka kuma, zai ci gaba da jaddada muhimmancin da Birtaniya ke bai wa bin doka, ƙa'idojin ƙasa da ƙasa, da kuma ƙungiyoyin duniya masu haɗa ƙasashe da dama, kamar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN).
Haka nan zai yi ƙoƙari ya tabbatar da ci gaban dangantaka ta musamman da ke tsakanin Birtaniya da Amurka. Sai dai ba lallai ba ne hakan ya kasance cikin sauƙi a dangantakarsa ta kai-tsaye da Shugaba Donald Trump, ko da yake babu shakka zai yi ƙoƙarin kyautata hulɗa da shi.
Dangane da ƙalubalen da Burnham ke fuskanta na zama firaiministan Birtaniya na bakwai cikin shekaru goma kacal, yawan sauyin shugabancin da aka gani a wannan ɗan gajeren lokaci shi kaɗai ya nuna irin babban aikin da ke gabansa. Sai dai akwai labari mai daɗi da kuma marar daɗi a gare shi.
Labari marar daɗin shi ne girman matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da suka gagari shugabannin shida da suka gabace shi.
Amma labari mai daɗi ga Burnham shi ne wataƙila farin jinin jam'iyyun da suka taso a matsayin masu adawa da tsarin siyasar gargajiya, wato Green Party da Reform, ya fara raguwa ko kuma ya kai matakin kololuwa wanda ba zai ƙara yawa ba – ko da yake ba a tabbatar da hakan ba.
A ƙarshe, akwai rashin tabbas mai yawa game da Burnham. Shin kamar yadda wasu ke tsoro, mutum ne mai fara'a amma marar nauyin siyasa da kwarewar shugabanci?
Ko kuwa kamar yadda 'yan majalisar Labour suke fatan gani, ko da yake da matakai daban-daban na fata, mutum ne mai cikakken hangen nesa da ƙwarewa wanda ke shirin zama babban ɗan siyasa kuma shugaba na ƙasa?
Wannan tambaya ce da lokaci ne kaɗai zai iya ba da amsa a kanta.