Kotu a Najeriya ta yanke wa wasu manyan jagororin ƙungiyar
Ansaru mai alaƙa da Al-Qaeda hukuncin ɗaurin rai da rai, bayan sun amsa
laifukan da suka shafi ta'addanci da ake tuhumarsu da su.
Mutanen da gwamnatin ƙasar ke zargin ta kama su ne tun a
watan Agustan 2025 kuma sun shafe watanni suna musanta zarge-zargen.
Mutanen biyu da ake zargi Mahmud Usman, wanda hukumomi
suka ce shi ne jagoran ƙungiyar Ansaru, da kuma Abubakar Abba, wanda ake zargi
dan shi ne mataimakinsa sun amsa dukkan
tuhume-tuhumen 32 da ake musu.
A zaman kotun na ranar Litinin, lauyansu Bala Dakum ya shaida
wa kotun cewa bayan tattaunawa da waɗanda yake karewa, sun amince da tuhume-tuhumen bayan sake karanto su a gaban kotu,
Hukumar SSS ta gurfanar da su a gaban kotu tun a watan
Satumbar 2025 kan tuhume-tuhumen da suka haɗa da ɗaukar nauyin ta'addanci, garkuwa
da mutane domin neman kuɗin fansa, haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, ƙera
bama-bamai na gida da kuma wasu laifuka masu alaƙa da ta'addanci.
Hukumar ta kuma zarge su da jagorantar ƙwayoyin ta'addanci a
ɓoye, da shirya hare-hare, da kuma alaƙa da ƙungiyoyin ta'addanci masu alaƙa da
Al-Qaeda da ke aiki a yankunan Sahel da Maghreb.
Mahmud Usman ya amsa cewa shi ne jagoran
Ansaru, yayin da su biyun suka amsa kasancewa mambobin ƙungiyar tare da shiga
garkuwa da mutane, haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba da sauran ayyukan
ta'addanci.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu
Ribadu, ya sanar da kama mutanen biyu ne tun a watan Agustan 2025 a wani samame
na haɗin gwiwar hukumomin tsaro bayan tattara bayanan sirri tsakanin watan Mayu
da Yulin shekarar.