Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 20 ga watan Yulin 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Sojojin Amurka uku sun mutu a kwana biyu sanadiyyar yaƙin Iran

    Rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta ce sojojinta uku sun mutu cikin kwanaki biyu sakamakon hare-haren Iran a rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin ƙasar da Iran.

    Rundunar ta ce, gaga cikin sojojin, biyu sun mutu ne bayan wani hari da aka kai kan sansanin sojin Amurka a Jordan ranar Juma’a, sannan wani soja ɗaya ya ɓace.

    Ɗayan sojan da ya mutu kuma ya mutu ne a arewacin Iraq ranar Asabar bayan wani hari da ake dangantawa da Iran.

    Rundunar ta kuma ce sojan da ya mutu a Iraq ya rasa ransa ne yayin wani aikin lalata ragowar wani jirgin yaƙi mara matuƙi na Iran da aka harbo.

    Haka kuma wani sojan Amurka guda ɗaya ya samu raunuka a lokacin

    A wani sabon bayani, CENTCOM ta ce an gano wasu gawarwaki da ba a tantance ko su waye ba a wurin harin da aka kai a Jordan, kuma ana ci gaba da bincike.

    Lamarin na zuwa ne yayin da Amurka da Iran ke ci gaba da musayar hare-hare a rana ta takwas a jere.

    A cikin kwanakin baya-bayan nan, ɓangarorin biyu sun zargi juna da kai hare-hare kan muhimman cibiyoyin more rayuwa. Amurka ta ce hare-harenta na baya-bayan nan na da nufin rage ƙarfin Iran wajen barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz tare da hukunta rundunar IRGC da take zargi da hannu a harin da aka kai Jordan.

  2. Harin Iran kan sansanonin sojin Amurka a Kuwait ya lalata muhimman kayan aikinsu

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta sanar a ranar Litinin cewa ta kai hari kan wasu wuraren sojin Amurka a Kuwait da jirage marasa matuƙa.

    A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce harin ya lalata na'urar Amurka na gano makamai a sararin samaniya gaba ɗaya.

    IRGC ta kuma ce ta kai hari kan wani rumbun adana kayan aiki da sassan jiragen sama, da kuma wurin ajiyar jiragen yaƙin MQ-9 na Amurka da ke sansanin Ali Al-Salem.

    Rundunar ta bayyana cewa harin martani ne ga hare-haren da Amurka ke ci gaba da kai wa Iran.

  3. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.