Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gasar Kofin Duniya: Spain ta lashe Kofin Duniya na 2026 bayan doke Argentina

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Wasan ƙarshe
Spain 1 , Argentina 0 Bayan karin lokaci
Spain
Argentina
After extra time
Gama Wasa Spain 0 , Argentina 0,Hutun rabin lokaci Spain 0 , Argentina 0

Muhimman abubuwa

Spain

  • Ferran Torres Goal 106 minutes extra time

Argentina

  • E. Fernández Two Yellow Cards 90 minutes plus 3
Ba da ƙwallo a ci
Spain,Nico Williams (106 minutes extra time)

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammad tare da taimakon AI

  1. Spain ta ɗaga Kofin Duniya na 2026, Bayan kammala wasa: Spain 1-0 Argentina

    Rodri ya ɗaga kofin sama a New Jersey yayin da kiɗa ke tashi.

    Shugaban Amurka Donald Trump na tsaye a gefe yana kallo.

  2. Rodri ya zama ɗan wasa mafi hazaƙa, Spain 1-0 Argentina

    Rodri ya tabbatar da matsayinsa na daya daga cikin manyan 'yan wasan tsakiya inda ya lashe ɗan wasa mafi hazaƙa a gasar.

  3. Simon ya lashe kyautar mai tsaron raga mafi ƙwazo, Spain 1-0 Argentina

    Mai tsaron ragar Spain Unai Simon ya zama mai tsaron raga mafi ƙwazo.

    Ya yi wasa bakwai ba tare da an zura ƙwallo a ragarsa ba kuma ƙwallo ɗaya kacal aka zura masa a ɗaukacin gasar.

  4. Cubarsi ya lashe matashin ɗan wasa, Bayan kammala wasa: Spain 1-0 Argentina

    Pau Cubarsi ya lashe kyautar matashin ɗanwasa mafi ƙwazo a gasar.

    Ɗan wasan mai shekaru 19! Yana murmushi har kunne.

  5. , Bayan kammala wasa: Spain 1-0 Argentina

    Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Fifa Gianni Infantino.

    Su ne za su gabatar da kyautuka.

  6. SPAIN TA LASHE KOFIN DUNIYA NA 2026, AN TASHI: Spain 1-0 Argentina

    Spain ta lashe kofin duniya na 2026 bayan doke Argentina.

    Ƴanwasan Spain ne suka fi taka rawar gani a wasan tun daga farko har zuwa ƙarshe.

    Gefe ɗaya ana hawayen farin ciki, a gefe ɗaya kuma ana hawayen bakin ciki.

    Lionel Messi yana zaune a filin wasa yana kallon abin da ke faruwa. Ko wannan ne lokaci na ƙarshe da za mu gan shi a Gasar Kofin Duniya?

    Lokaci ne kawai zai tabbatar.

    A halin yanzu, wannan lokaci ne na Spain.

  7. Argentina ta kai hare-hare masu haɗari, Spain 1-0 Argentina

    Argentina na ta dagewa domin ganin ko za ta farke.

  8. An ƙara minti biyar, Spain 1-0 Argentina

    Nan da minti biyar Idan Argentina ba ta yi wani kyakkyawan motsi ba Spain za ta lashe kofin duniya na 2026.

  9. , Spain 1-0 Argentina

    Lionel Messi ya doki wata ƙwallo da ƙarfi a bakin da'irar Spain amma ta sha Merino a fuska.

    Sai da aka ɗauki mintuna ana ba shi kulawa kafin ya miƙe.

  10. , Spain 1-0 Argentina

    Ƴan wasan Argentina sun fara fitowa, to amma dai abin da wahala ksancewar an kori ɗanwasansu ɗaya.

  11. Ƙwallo a raga: Spain ta jefa ƙwallo a ragar Argentina, Minti na 107: Spain 1-0 Argentina

    Ferran Torres ne ya jefa ƙwallo a ragar Argentina.

  12. An dawo daga hutu, Spain 0-0 Argentina

  13. An je hutu, Spain 0-0 Argentina

    An je hutu a cikin ƙarin lokaci kuma har yanzu babu ci tsakanin tawagogin biyu.

    Amma dai Spain ce ke ci gaba da nuna ƙwarewa a wannan wasa.

  14. Ƙiris Merino ya jefa ƙwallo a raga, Spain 0-0 Argentina

    Chris Sutton, tsohon dan wasan gaba na Ingila a BBC Radio 5 Live a filin wasa na New York New Jersey

    Ta yaya Mikel Merino ya gaza jefa wannan ƙwallo a raga? Wanda ya zura kwallaye masu kyau ga Spain a wannan gasar cin kofin duniya. Ya sa mata kai amma ta bauɗe, ƙiris ta shiga.

  15. , Spain 0-0 Argentina

    Spain na ci gaba da matsa wa Argentina.

  16. SPAIN TA CI AN SOKE, Spain 0-0 Argentina

    Nico Williams ne ya zura wallo a raga amma lafari ya ce akwai fawul..

  17. An fara wasa a arin lokaci, Spain 0-0 Argetina

  18. LOKACI YA CIKA, Spain 0-0 Argentina

    Lokaci ya cika ana 0-0.

    Yanzu za a je ƙarin lokaci.

    Ko Argentina za ta iya da ƴanwasa 10?

    Lokaci ne zai tabbatar.

  19. An bai wa ENZO jan kati, Spain 0-0 Argentina

    Enzo Fernandez ya yi wa Pau Cubarsi mummunar ƙeta.

    Dama yana da katin gargaɗi, yanzu an ƙara masa wani, kora ke nan.

    Aiki ya ƙara jiƙe wa Argentina.

  20. , Spain 0-0 Argentina

    Aymeric Laporte ya ɗauke Lionel Messi.

    Argentina ta samu bugun tazara, abu ɗaya da suka yi domin burge magoya bayansu.