Yadda cacar baki ta kaure tsakanin APC da Kwankwaso akan matsalar tsaro

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Asalin hoton, others

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta mayar da zazzafan martani akan kalaman da aka jiyo daga bakin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jama'iyyar NDC, kuma tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya ƙalubalanci salon kamun ludayin gwamnatin shugaban ƙasar Bola Tinubu, musamman kan mastalar tsaro da ake fama da shi a ƙasar.

Yayin wata hira da kafar talabijin ta Channels, Kwankwaso, ya zargi gwamnatin APC da yin wasarere da rayukan ƴan Najeriya, da kuma gaza shawo kan matsalar tsaro, da tattalin arziki da kuma tashin farashin kayan masarufi.

Yayin hirar da aka yi da Sanata Kwankwaso, ya kuma zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da bijiro da wasu tsare tsare da ke jefa ƴan ƙasar cikin halin ni ƴasu, da kuma uwa uba yadda a kusan kullum ake samun asarar rayukan ƴan ƙasar a dukkan sassan Najeriya, abin da a cewarsa ya zama wajibi ƴan Najeriyar su tashi tsaye don ƙwatarwa kansu ƴanci a zaɓen da ke tafe.

Daraktan watsa labarai na jam'iyyar APC Malam Bala Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa, wannan yarfe ne kawai na siyasa, da Kwankwason ke yi don neman ƴan Najeriya su goya musu baya a zaɓen 2027.

Ya ce,"Dukkan abubuwan da Kwankwaso ya faɗi da ma sukar da ya yiwa manufofin jam'iyyarmu, ai ya yi gwamna har sau biyu, sannan ya yi ministan tsaro, don haka ya san matsalar tsaro, domin tun a lokacin da ya yi gwamna matsalar tsaron na nan, haka lokacin da ya yi minista ma matsalar na nan, a don haka su kan faɗi wasu abubuwa ne don jin daɗin bakinsu ba wai don gwamnatin APC ba ta yin wani abu ba."

"Idan da a ce su Kwankwason sun yi wa tufkar hanci, ma'ana sun magance matsalar tsaron a lokacin da suke da shugabanci don daga hannunsu muka ƙwaci mulki saboda rashin iyawa." In ji shi.

Bala Ibrahim, ya ce,"A duk lokacin da aka fito da matakai na gyara, akwai waɗanda suke ɓarna ko kuma suke cin moriyar ɓarnar don haka ba za su ji daɗi ba, don haka sai su rinƙa zuga waɗanda ake yin gyaran dominsu don kada su nuna soyayya da wannan gyara da ake musu."

To sai dai duk da irin waɗannan kalamai da APC ke yi, makusantan sanata Kwankwaso na ci gaba da kafewa a kan cewa kalaman ɗan takarar nasu, na kan hanya.

Dr Habibu Saleh Mai Lemo, shi ne kakakin ƙungiyar Kwankwasiyya ta sanata Kwankwaso, ya shaida wa BBC cewa, ai haƙƙin kowacce gwamnati na farko shi ne kare rayuka da dukiyoyin al.'ummarta.

Ya ce."Duk wani ɗan Najeriya a yanzu zai tabbatar da cewa a yanayin da ake a yanzu a kowane ɓangare na ƙasar an tabbatar da cewa akwai gazawa daga gwamnatin Tinubu, kuma duk ɗan Najeriya na da haƙƙin sanin abin da ke faruwa a ɓangaren tsaro."

Sau tari dai ƴan hamayya a Najeriya kan fito su furta kalamai irin waɗannan na nuna gazawar gwamnati, da ita kuma gwamnatin ke cewa suna yinsu ne don gyara miyarsu ta siyasa kawai ba wai tsakani da Allah ba, ko da yake masu sharhi na cewa adawa irin wannan ce gishirin dimukraɗiyya da ya kamata gwamnati ta riƙa saurara don toshe ƙofar matsalolin da ake nuna mata.