Chelsea, Arsenal da Spurs na zawarcin Rashford, Arsenal na son Konsa

Marcus Rashford,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marcus Rashford
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tottenham, da Chelsea da Arsenal na zawarcin ɗan wasan Manchester United Marcus Rashford, sai dai United din ba ta son siyar da shi ga wata ƙungiya da ke Ingila. (The I - subscription required)

Mai tsaron ragar Aston Villa da Arjantina Emiliano Martinez, 33, ya kasnace mai tsaron ragar da Juventus ke hari, yayin da Arsenal ke son ɗauko ɗan wasan Aston Villar da Ingila Ezri Konsa. (Telegraph - subscription required)

Nottingham Forest sun shiga mataki na gaba kan tattaunawa da ɗan wasan Sporting CP da Ivory Coast Ousmane Diomande, 22. (Fabrizio Romano)

Juventus na son ɗauko ɗan wasan West Ham's da Fransa Jean-Clair Todibo. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Manchester United na kan aniyar ta na ɗauko sabon dan wasan tsakiya, sai dai sun sassauta kan son siyen ɗan wasan Brighton da Kamaru Carlos Baleba da dan wasan Bournemouth Guernseyman Alex Scott, saboda tsadar farashin da suka sa musu. (Teamtalk)

Bournemouth na kan shirin ta na ci gaba da riƙe Scoot, da Arsenal ke son ɗauka, duk da cewar dan wasan Ingilan ya yi wasti da tayin kwantaragin da Bournemouth ɗin ta yi masa. (Telegraph - subscription required)

Ipswich ta amince da tayin daukar dan wasan Celtic da Japan Daizen Maeda, kan fam miliyan 8, da kwantaragin tallah na fam miliyan 2. have agreed a deal in principle to sign Celtic's Japanese forward Daizen Maeda, 28, for £8m plus £2m in add-ons. (Sky Sports)

Rangers da karin wasu ƙungiyoyi da ke Asutraliya na sa ido kan ɗan wasan Australiya da Manchester United James Overy. (Mail Plus - subscription required)