Messi, Maradona ko Pelé - wane ne gwarzon ɗanwasan duniya?

    • Marubuci, Giulia Granchi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da Lionel Messi ke shirin buga wasan ƙarshe na gasar kofi duniya a karo na uku a rayuwarsaa, wata tambaya da aka saba yi ta dawo: Shin zaƙaƙurin ɗanwasan Aregentinan fi kowa zarra a tarihin ƙwallon ƙafa? Ya zarce dan ƙasar shi, Diego Maradona da kuma ɗan Brazil Pele?

Messai mai shekara 39, ya zamo ɗanwasan Argentina da ya fi ɗaukar hankali a gasar kofin duniya ta 2026.

Masu sharhi sun ce duk da a yanzu ana iya cewa ya wuce zamanin tashen shi, Messi na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen samun sakamako a wasanni ta hanyar jan ragamar sauran yanwasan tawagar tamkar wani koci na cikin fili.

Ko ana iya cewa ya zarce abokan hamayyar shi?

Bayyanar Messi

Masu cewa Messi ne ya fi kowanne ɗanwasa a tarihin ƙwallon ƙafa suna kafa hujja ne da dalilai guda biyu: Ƙarkon da ɗanwasan ya yi yana jan zaren shi da kuma bayar da sakamako a lokacin da ake buƙata.

Ba kamar yadda tauraruwar ƴanwasa ta saba dushewa da zarar sun yi tashe na ɗan gajeren lokaci ba, Messi ya shafe kusan shekara 20 yana jan zaren shi a wasan ƙwallo.

A cikin waɗannan shekarun, ya lashe kyautar gwarzon ɗanwasa ta Ballon d'Or har takwas, ya ci gasar ƙasashen Sifaniya da Faransa, da gasar zakarun Turai da Copa America da kuma kofin duniya a 2022, yayin da ya kafa wani tarihin a fannin cin ƙallaye da yawa.

Masu goyon bayan shi suna kuma nuna ƙwarewar shi wajen iya taka leda a duk inda ya samu kanshi, daga yadda Barcelona ta mamaye Turai zuwa kane-kanen da Argentina ta yi a fagen ƙwallon ƙafa a duiya.

Masoyan Messi su na ganin ƙarkon da ya yi, da basirar shi da gudunmuwar da ya ke bayarwa wajen samun nasarar ƙungiyoyin shi, su ne banbancin shi da sauran ƴanwasa da aka yi a tarihi.

Tsohon ɗanwasan Fransa, Thierry Henry ya zayyana wasu abubuwa na musamman kan tsohon abokin taka ledar shi a Barcelona.

A wata hira da jaridar Sifaniya Marca, Henry ya tuna yadda a lokacin, da zarar an tunzura Messi to shi kenan ''an kira ruwa'' don kuwa nan take yake canza akalar wasa.

Tasirin sunan Maradona

A Argentina, idan ana kwatancen ƴanwasa ba a mayar da hankali kan Pele da sauran manyan ƴanwasa da suka yi fice a duniya, don kuwa an fi mayar da hankali ga Diego Maradona, kyaftin ɗin ƙasar da ya jagoranci ƙungiyar da ta lashe kofin duniya a 1986.

Tasirin Maradona ya wuce ƙwallon ƙafa. Ga ƴan Argentina da yawa, ya zama wani jigo na haɗin kan ƙasa.

"Maradona sarki ne a Argentina. Ba a zaɓen sarki, shi zaɓi ne ba na wasu mutane ba kuma wakilin ƙasa ne baki ɗaya,'' in ji ɗanjaridar Sifaniya, Guillem Balagué, ɗaya daga cikin waɗanda suka rubuta tarihin Messi.

Shekaru da dama, wasu ƴan Argentina na matuƙar ƙaunar Messi, amma duk da haka suna kallon Maradona a matsayin wanda ya fi dacewa a kira jagora a ƙasar.

Maradona wanda ya rasu a 2020, ya tashi ne a cikin talauci amma ya fito ƙarara ya ƙalubalanci mahukunta inda ya shiga harkokin siyasa, tare da samun goyon bayan jama'a.

A nasa ɓangaren Messi ya zaɓi ya zama na daban, ba ya shiga harkar siyasa kuma babu ruwan shi da duk wani abu da ba wasan ƙwallo ba.

How Messi changed perceptions

Martabar Messi ta ƙaru bayan Argentina ta lashe Copa America a 2021, ta kawo ƙarshen jiran shekara 28 ba tare da ta lashe gasar ƙwallon ƙafa ba.

Tasirin shi ya ƙaru a gasar kofin duniya ta 2022, inda ya taimakawa Argentina ta lashe gasar karo na uku.

A lokacin gasar Messi ya nuna ƙwarewa a fanni jagoranci da tafiya tare da kowa, lamarin da a baya magoya bayan ƙungiyar ke ganin cewa Maradona ne kawai zai iya yi.

"Ya nuna sabon salo na ƙwarjini," in ji Balagué. "Daga nan mutane suka fara kallon shi a matsayin wani janar a cikin tawagar."

Ƴan Argentina da dama na ganin cewa daga lokacin Messi ya zarce Maradona a tasirin ƙwallon ƙafa a ƙasar.

Tsakanin Messi da Pelé

Wasu masu sharhi na ganin cewa ba Maradona kaɗai Messi ya yi wa zarra ba, har ma da Pelé, gwarzon ɗanwasan Brazil da ake wa laƙabi da ''Sarkin Ƙwallon ƙafa'', wanda ya rasu a 2022.

Pelé ya kasance ɗanwasa ɗaya tilo da ya taɓa lashe kofin duniya sau uku, inda ya taimakawa Brazl ta ci kofin a 1958 da 1962 da kuma 1970.

A wata hira da jaridar Folha de S.Paulo, ta yi da shi a 2018, Pelé ya ce Maradona ya zarce Messi nesa ba kusa ba. Ya ce Messi ya dogara ne ga ƙafar shi ta hagu kacal, don haka ba ya cikin zaratan ƴanwasan da ake kira ''sun cika kowacce ƙa'ida ta ƙwarewar taka leda''.

"[Franz] Beckenbauer da [Johan] Cruyff ma sun zarce Messi," in ji Pelé.

Tsohon ɗanwasan Brazil, Tostão ya kalli abin daga wata mahanga ta daban. A 2021, ya ce Messi ya zarce Maradona amma har yanzu bai kamo gwarzon Brazil, Pelé ba.

"Bayan Pelé, Messi ne gwazon ɗanwasan da ya zarce kowa a tarihi," in ji Tostão.

Ƙarin bayani

To request:

Complete the translations here: https://tinyurl.com/bdevvs6r

Fill-in the commissioning form https://bit.ly/ws_design_form with this title in English: Pelé Maradona and Messi comparison - 2026071602

Bayanan da kea ƙasa na nuni da cewa da ƙididdigar kofuna da ƙwallaye kawai ake bi wajen tantance wanda ya fi gawurta da yanzu wannan muhawara ta ƙare.

Messi ya tara kyautuka da abubuwan tarihi a matsayin shi da kuma matakin ƙungiyoyi ta yadda ba wanda ya kama ƙafar shi a wannan fannin.

Amma waɗannan lambobi kaɗai ba za su iya tantance ɗanwasan da ya zama gagarabadau ba a ƙwallo. Don haka ake ci gaba da wannan muhawara.

Wani abu da ya sanya wannan muhawara ta ƙara zama mai wahala shi ne: Pelé da Maradona da kuma Messi sun yi tashe ne a zamani daban-daban.

Lokacin da Pelé ya lashe kofin duniya a karon farko a 1958, babu fasahar zamani ta yaɗa wasanni ƙwallo cikin sauƙi.

Ya zuwa zamanin Maradona a shekarar 1980, wasan ya gawurta har ya zamo wata ma'aikata da ake juya biliyoyin dala.

Messi kuwa ya zo a lokacin da akwai kayan aikin zamani na tantance duk wani salo da ya yi a fili, da tsarin kiwon lafiya mai inganci kuma ga fasahar zamani da ke taimakawa wajen yanke hukunci kan duk abin da ya faru a filin wasa.

Saboda haka kwatanta waɗannan ƴanwasa abu ne mai wahalar gaske.

Domin haka da wuya a iya kawo ƙarshen wannan muhawara ta gano ɗanwasan da ya zarce kowa zaƙaƙuranci a tarihi.

Graphic by Caroline Souza and Laís Alegretti, BBC News Brasil