BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Badaƙalar kuɗi 5 da suka shafi kamfanin man fetur na Najeriya
Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ya sha fuskantar zarge-zargen badaƙalar kuɗi a tsawon shekaru, daga zargin ɓacewar kuɗin sayar da man fetur zuwa zargin badaƙalar tallafin man fetur.
Milan na zawarcin Spence da Romero, Liverpool ta dage kan Sano
Inter Milan na tattaunawa kan sayen Djed Spence da Cristian Romero, yayin da Liverpool ke kan gaba wajen neman Kaishu Sano, ita kuwa Arsenal na son Ezri Konsa ne.
Amfani shida da Sallah ke da su ga lafiyar mai yin ta
Baya ga lada da kusanci ga Ubangiji, masana lafiya sun alaƙanta ta da inganta lafiya da tsaftar jiki.
Ko ratse wa Mashigar Hormuz za ta magance tsadar fetur a duniya?
Mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigila ta ruwa a duniya, wadda ta ƙara jan hankalin duniya musamman bayan ɓarkewar yaƙi a tsakanin Iran da Amurka.
Jami'an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da ceto ɗaliban da shugaban makarantar da wani jami'in NECO a sanarwa da ya fitar.
Iran ta zargi Amurka da aikata laifukan yaƙi
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 16/07/2026
Abu 5 da kake buƙata don zama ɗansanda a Najeriya
Ƴansandan za su gudanar da tantancewa da kuma gwaje-gwajen lafiya a kan masu neman zama ɗansadan da zarar sun isa kwalejin horarwar kuma nan take ake sallamar wadanda suka gaza tsallake gwajin da tantancewar.
Majalisar wakilan Amurka ta dakatar da dukkan tallafin da ake bai wa Najeriya
A baya ƙudurin ya bai wa Amurka damar riƙe kashi 50% ne na tallafin, amma a yanzu majalisar ta ƙara shi zuwa kashi 100%.
Abubakar Malami: Jerin kadarori 48 da aka ƙwace daga tsohon ministan shari'a
EFCC ce dai ta shigar da ƙara ta buƙatar ƙwace kadarorin tsohon ministan guda 57 na dindindin da darajarsu ta kai naira biliyan 212.8.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 17 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 16 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 16 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 16 Yuli 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Sakamakon wasannin Gasar Kofin Duniya 2026
Dukkanin bayanan da suka kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026
Wasanni
Dalilai uku da ke bai wa Argentina damar farke ƙwallaye har ta ƙara
Argentina mai rike da kofin duniya ta zo da wani salo a gasar cin kofin duniya 2026, inda ake zura mata ƙwallo a raga, amma sai ta farke ta kuma kai zagayen gaba. Shin menene dalilin hakan? Mohammed Abdu ya tsara mana rahoto kan wannan.
Me ya sa rashin nasarar Ingila a hannun Argentina ta zama mafi raɗaɗi?
Shekarun baƙin cikin Ingila yanzu za su wuce 60, na rashin lashe kofin duniya, amma rashin nasara a hannun Argentina a wasan daf da karshe, zai kasance mafi muni da raɗaɗi a Gasar Kofin Duniya da ta buga.
KAI TSAYE, Ko Alvarez zai koma Arsenal? Sunderland ta ɗauki Thomas Meunier
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labarin wasanni kai tsaye tare da sharhi da bayanan abubuwan da ke wakana a fannin wasanni a faɗin dunita
Man United na son Summerville, Arsenal za ta taya Nusa
Danwasan West Ham, Crysencio Summerville, na cikin wadanda Man United ke son dauka, yayin da Arsenal ke shirin taya danwasan RB Leipzig Antonio Nusa na Norway.
Gasar Kofin Duniya: Argentina ta kai wasan karshe bayan doke Ingila 1-2
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku kai tsaye wasan England da Argentina a zagayen daf da karshe a gasar cin kofin duniya tare da sharhi da bayanai
Mutumin da ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin Gasar Kofin Duniya
Tarihin Just Fontaine na zura ƙwallaye 13 a gasar kofin duniya guda ɗaya da ya buga ya daɗe ba tare da an karya ba. Amma bai sake taka leda a gasar ba, saboda raunin da ya ji da ya kawo ƙarshen sana’arsa ta ƙwallon ƙafa tun yana da shekaru 28 da haihuwa.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Shari'o'i huɗu da jam'iyyar ADC ke fuskanta gabanin zaɓen 2027
Rikicin da ya dabaibaye ADC ya fi karkata ne kan tambayar waye ke da ikon jagorantar jam'iyyar da kuma tsare-tsarenta domin fuskantar babban zaɓen da ke tafe.
Yankuna 5 da suka fi haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa a Najeriya
Akwai wasu yankuna da ake yawan samun ambaliyar ruwa saboda yadda suke kusa da manyan koguna da madatsun ruwa, ko kuma saboda ruwa da ake saki daga wasu manyan madatsun da ke cikin Najeriya da ƙasashe maƙwabta.
Yadda Trump ya shiga tsaka mai wuya wajen kawo ƙarshen yaƙi da Iran
Sabuwar buƙatar da Donald Trump ya gabatar game da yaƙin Iran ta daɗe ne na sa'o'i 24 kacal, kuma ta nuna shugaban ƙasa da ke neman hanyoyi marasa al'ada domin fita daga wani mawuyacin hali.
Yadda ake muzguna wa direbobi don bayar da cin hanci a Najeriya
Masu harkokin sufuri a Najeriya sun yi zargin cewa, hanyoyin kasar sun zame masu wani waje da ake tilasta musu bayar da makudan kudade a duk rana matsayin cin hanci.
Iran ta ce ta kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Kuwait
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 15/07/2026
Yadda Erdogan ya sauya fasalin Turkiyya cikin shekara 10
Abubuwan da suka biyo bayan yunƙurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yulin 2016 sun sauya duk wasu fannonin siyasar Turkiyya cikin shekara 10 da suka gabata, lamarin da ya sauya abubuwa a cikin gida da kuma waje.
Ko sheƙa gudu a mota na sawa mu isa inda za mu je da wuri?
Duk da cewa a zahiri mukan yanke hukuncin ƙara gudun abin hawa a duk lokacin da muke sauri, wani nazari da aka yi zai iya sawa ka sauya tunaninka game da hakan.
Abin da muka sani kan yadda Boko Haram da ISWAP 'ke amfani da AI'
"Ana kuma amfani da kyamarori da ke haɗe da fasahohin AI wajen nazarin abubuwan da suka faru bayan kai hari. Wannan na ba mayaƙan damar fahimtar kurakuran da suka tafka da kuma hanyoyin inganta hare-haren da za su kai a gaba."
Wace riba Tinubu ke samu daga takarar Muslim-Muslim?
A ƙarshen makon da ya gabata ne jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya zaɓi mataimakinsa Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a zaɓen 2027, bayan miƙa sunayensu ga hukumar INEC.
'Muna ta roƙon gwamnati ta ceto yaranmu amma shiru' - Iyayen ɗaliban Borno
Ɗaya daga cikin iyayen, Bukar Buba, ya shaida wa BBC cewa suna cikin "baƙin ciki da takaici", ganin cewa har yanzu ƴaƴansu na hannun masu garkuwa da mutane duk da cewa an saki waɗanda aka sace a Oyo.
Mene ne takamaiman abin da Amurka ke buƙata daga Iran?
Wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka, sun ambato wata majiya daga jami'an Amurka na cewa, a asirce, Iran ta amince cewa ta yi kuskure da ta kai hari kan jiragen ruwa da ke bi ta mashigar.
Dalilan da suka sa tattalin arzkin China ya fuskanci koma-baya a bana
Alƙaluman kan yawan abin da ƙasa ke samarwa sun nuna cewa tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da kashi 4.3 cikin 100 a rubu'in shekara na biyu, adadin da ya gaza cimma burin da gwamnatin Beijing ta sa a bana
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.
































































