Jami'an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Asalin hoton, Usman Ododo/X
Gwamnatin jihar Kogi ta ce jami'an tsaro sun ceto mutum huɗu da aka sace yayin wani hari da ƴan bindiga suka kai wata makaranta a ƙaramar hukumar Dekina.
An sace ɗaliban ne tare da shugaban makarantar da kuma wani ma'aikacin wucin gadi na hukumar shirya jarabawar NECO a ranar Talata, bayan da wasu ɗauke da makamai suka kai hari makarantar da ke Odo-Ekina.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ne ya tabbatar da ceto mutanen a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce an ceto su ne bayan wani samame na haɗin gwiwa da jami'an tsaro suka ƙaddamar bisa umarnin gwamna Usman Ododo.
"Mun tabbatar da cewa an saki shugaban makarantar da jami'in NECO da kuma ɗaliban biyu, kuma duk suna cikin ƙoshin lafiya," in ji sanarwar.
Fanwo ya ƙara da cewa halin yanzu suna hannun jami'an tsaro domin ɗaukar bayanansu da kuma yi musu gwaje-gwajen lafiya da suka kamata.
Ya kuma ce: "Har yanzu jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da samame a cikin dajin domin kamo waɗanda suka kai harin."




































