Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 15/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 15/07/2026

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Tattaunawar Lebanon da Isra'ila ta ƙare ba tare da cimma matsaya kan janye sojoji ba

    Jami'an Lebanon da Isra'ila sun kammala wata tattaunawa ta bayan fage da Amurka ta shirya a birnin Rome na Italiya, ba tare da cimma matsaya kan takamaiman lokacin da sojojin Isra'ila za su fice daga kudancin Lebanon ba.

    A wata yarjejeniya da ɓangarorin suka fitar a watan da ya gabata, sun amince da fara janyewar Isra'ila daga wasu yankuna na farko a kudancin Lebanon.

    Yarjejeniyar ta kuma tanadi kwance ɗamarar ƙungiyar Hezbollah, da kuma maye gurbin sojojin Isra'ila da dakarun gwamnatin Lebanon a yankunan da abin ya shafa.

    Sai dai wakilin BBC ya ce jami'an Lebanon sun nuna rashin gamsuwa da sakamakon tattaunawar, saboda suna ganin ba za a samu wani ci gaba ba kafin gudanar da zaɓen Isra'ila da ake sa ran yi a watan Oktoba.

  2. Faransa ta amince da tsarin taimaka wa mara lafiya ya mutu

    Macron

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dokokin Faransa ta amince da wani ƙudiri da zai ba da damar taimaka wa wasu marasa lafiya su mutu.

    Sai dai tsarin zai kasance ƙarƙashin tsauraran sharuɗɗa ne.

    An shafe shekaru ana muhawara kan batun, duk da cewa Majalisar Dattawan ƙasar ta yi watsi da shi har har sau uku a baya.

    Idan ƙudirin ya zama doka, zai shafi manyan mutane da ke fama da cuta mai tsanani kuma marar magani, wadda ta kai matakin ƙarshe ko kuma take jefa su cikin matsananciyar azaba ko rikita musu tunani ta yadda magani ba ya iya rage raɗaɗin da suke ji.

    Ƙudirin ya tanadi cewa mara lafiyar ne zai sha maganin da zai kawo ƙarshen rayuwarsa da kansa.

    Amma idan yanayinsa bai ba shi damar yin hakan ba, likita ko mai jinyarsa na iya taimaka masa wajen aikata hakan.

    Sai dai kafin ƙudirin ya zama doka, za a miƙa wasu sassa nasa ga majalisar kare kundin tsarin mulkin Faransa domin ta tantance ko sun yi daidai da kundin tsarin mulkin ƙasar.

  3. EU za ta tallafawa Venezuela da dala miliyan 23

    Venezuela

    Asalin hoton, Getty Images

    Tarayyar Turai ta sanar da ƙarin tallafin jin ƙai na kusan dala miliyan 23 ga Venezuela, domin taimakawa waɗanda girgizar ƙasar da ta afku a watan da ya gabata ta shafa.

    EU ta ce za a ware kusan rabin kuɗin ne domin kai agajin gaggawa ga mutanen da ibtila'in ya fi shafa, yayin da sauran rabin za a yi amfani da shi wajen tallafa wa ɓangaren lafiya da sauran muhimman ayyukan jin kai.

    Gwamnatin riƙon ƙwarya ta Venezuela ta ce girgizar ƙasar ta yi sanadin mutuwar sama da mutum 4,700, tare da haddasa mummunar asara ga rayuka da dukiyoyi a sassa daban-daban na ƙasar.

  4. Iran ta ce ta kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Kuwait

    Iran ta ce ta kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Kuwait

    Asalin hoton, Getty Images

    Gidan talabijin na gwamnatin Iran, IRIB, ya ruwaito cewa Iran ta kai hari kan wani sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Kuwait.

    A cewar kafar yaɗa labaran, an kai harin ne a tsibirin Bubiyan, wanda shi ne mafi girma a Kuwait.

    Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta bayyana harin a matsayin "martani mai ƙarfi" daga Iran.

    Kafar ta kuma ce an ji wasu manyan fashe-fashe a wasu wuraren da ta ce hedkwatar ƙungiyoyin adawar Iran ne, waɗanda ta bayyana a matsayin "ƙungiyoyin ta'addanci".

    A cikin watannin baya-bayan nan, Iran ta sha kai hare-hare kan sansanonin ƙungiyoyin Kurdawan adawa da ke yankin Kurdistan na ƙasar Iraki.

    Sai dai har zuwa yanzu, ba a samu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da kai harin kan sansanin sojin Amurka da ke Kuwait ba.

  5. Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Najeriya 14

    Madatsar ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da madatsun ruwa ta Najeriya (NIHSA) ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a samu ambaliya a wasu sassan jihohi 14 na ƙasar tsakanin 14 zuwa 20 ga watan Yuli.

    Darakta Janar na hukumar, Umar Mohammed, ya ce hasashe ya nuna akwai yiwuwar koguna su cika bayan rahotannin da hukumar ta samu.

    Ya ce daga cikin wuraren da aka fi sa ran ambaliyar za ta iya shafa akwai Saminaka da ke kusa da kogin Karam da yankin madatsar Waya ta kogin Waya, da kuma Amber da ke ta wajen kogin Amber.

    Jihohin da NIHSA ta ce za su iya fuskantar matsakaicin haɗarin ambaliya sun haɗa da Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Benue, Borno, Cross River, Edo, Enugu, Imo, Kaduna, Legas, Neja da kuma Filato.

    Hukumar ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan kariya ba, ambaliyar na iya shafar al'ummomi da dama tare da lalata muhimman wurare kamar makarantu, cibiyoyin lafiya, kasuwanni da sauran ababen more rayuwa.

    Saboda haka, NIHSA ta buƙaci mazauna yankunan da aka fi fargabar ambaliya su koma wurare masu aminci, su kuma riƙa share magudanan ruwa, su guji bi ta hanyoyin da ruwa ya mamaye, sannan su riƙa bibiyar sanarwar hasashen ambaliya da hukumar ke fitarwa.

    Hakazalika, hukumar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da hukumomin bayar da agajin gaggawa su kasance cikin shirin ko ta kwana da shirye-shiryen kwashe jama'a daga yankuna masu haɗari da kuma wayar da kan al'umma.

  6. Kotu ta bayar da umarnin ƙwace kadarori fiye da 40 masu alaƙa da Malami

    Abubakar Malami

    Asalin hoton, Abubakar Malami

    Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ƙwace kadarori kusan 48 da ake alaƙanta su da tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami.

    Mai shari'a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin bayan ta amince da buƙatar da Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci ta gabatar, inda ta ce waɗanda suka yi iƙirarin mallakar kadarorin sun kasa tabbatar wa kotu cewa sun mallake su ne ta hanyar da ta dace.

    Mai shari’ar ta ce batun da ke gaban kotun ba wai na tantance wanda ya mallaki kadarorin ba ne, ana shari’a ne kan tantance ko kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen sayen kadarorin ko sun fito ne ta halastacciyar hanya.

    Daga cikin kadarorin da za a ƙwace har da gidan rediyon Rayhan da jami'ar Rayhan da wasu otal-otal da kamfanoni da rukunin gidaje na alfarma.

    Abubakar Malami

    Asalin hoton, EFCC

    Abubakar Malami

    Asalin hoton, EFCC

    Ta ƙara da cewa waɗanda ake ƙara sun kasa gabatar da gamsasshiyar hujja cewa sun mallaki kadarorin ne da kuɗaɗe halastattu.

    Kafin yanke hukuncin, kotun ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafe da buƙatun da Malami da wasu daga cikin 'yan uwansa da kuma wasu kamfanoni masu alaƙa da kadarorin suka gabatar, inda suka nemi a soke umarnin ƙwace kadarorin na wucin gadi da aka bayar tun da farko.

    Abubakar Malami

    Asalin hoton, EFCC

    Sai dai kotun ta ƙi amincewa ta bayar da umarnin ƙwace wasu daga cikin kadarorin da EFCC ta gabatar.

    Tun da farko hukumar ta nemi a ƙwace kadarori 57 ne, amma kotun ta amince da ƙwace kusan 48 daga cikinsu.

    Mai shari’a ta dogara da tanadin Sashe na 17 na Dokar almundahana da sauran laifuka wajen yanke hukuncin.

    Sai dai kotun ta bayyana cewa wannan hukuncin na ƙwace kadarori ba yana nufin an same Malami ko wani daga cikin iyalansa da laifin aikata laifi ba domin shari'ar ƙwace kadarori ta sha bamban da shari'ar aikata laifi.

    Abubakar Malami

    Asalin hoton, EFCC

  7. Kotun Kenya ta haramta wa mabiya addinin Rastafariya shan wiwi

    Wata kotun Kenya ta ƙi bai wa mabiya addinin Rastafariya 'yancin shan wiwi bisa dalilai na addini.

    Masu shigar da ƙarar sun ce tabar wiwi na taka muhimmiyar rawa a wajen gudanar da ibadarsu, kuma haramta amfani da ita ya saɓa wa haƙƙinsu na kundin tsarin mulki na ƴancin gudanar da addini.

    Alƙalin kotun ya ce ƴan Rastafariyar sun kasa gabatar da gamsassun hujjoji da za su tabbatar da cewa amfani da wiwi wani ginshiƙi ne wajen gudanar da addinin nasu.

  8. Ukraine da EU za su yi aiki tare don ƙera jirage marasa matuƙa

    Ukraine da Tarayyar Turai sun amince da ƙaddamar da ayyukan haɗin gwiwa domin ƙara yawan ƙera jiragen yaƙi marasa matuƙa.

    Da take jawabi a birnin Kyiv, shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta ce yarjejeniyar za ta haɗa ƙwararrun Ukraine wajen ƙera irin waɗannan jirage da kuma amfani da ƙarfin masana’antun Turai.

    Ta ce Ukraine ta ƙware sosai wajen ƙera jirage marasa matuƙa tun bayan mamayar Rasha kuma ta sayar da fasaharta ga ƙasashe tara ciki har da wasu daga cikin ƙasashen Gabas ta Tsakiya da ke neman hanyoyi masu rahusa na kare kansu daga hare-haren Iran.

    Mrs Ursula von der Leyen ta ce dole ne Turai ta haɗa kai domin cimma nasara saboda sanin irin barazanar da dukkan ƙasashen ke fuskanta.

    Wannan dai ita ce yarjejeniya ta farko da aka tsara za ta haɗa ƙasashe da kamfanoni a faɗin Tarayyar Turai wajen samar da irin waɗannan jirage.

  9. Ko Ingila za ta iya ɗaukar fansa kan Argentina?

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  10. Ƴantawayen Houthi sun harba makamai cikin Saudiyya

    Ƴantawayen Houthi sun harba makaman linzami zuwa cikin Saudiyya bayan da suka zarge ta da kai hari kan filin jirgin da ƙungiyar ke iko da shi, wani mataki da ƙungiyar ta ce ya saɓa wa ƙa'idar yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekara huɗu da suka ƙulla.

    Harin ya kawo ƙarshen yarjejeniyar zaman lafiya da ɓangarorin biyu suka cimma, lamarin da ya haifar da fargabar Iran za ta yi amfani da ƙungiyar ta Houthi wajen rufe mashigar Bab al-Mandab.

    Bab al-Mandab na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin fito na duniya mafiya muhimmanci da ta ratsa Tekun Maliya.

    Toshe mashigar zai iya haifar mummunan koma-baya ga cinikayyar ruwa ta duniya, bayan toshe mashigar Hormuz.

  11. Najeriya ta kammala kwashe ƴanƙasarta daga Afirka ta Kudu

    Ƴan Najeriya

    Asalin hoton, TOYIN ADEDOKUN / AFP via Getty Images

    Hukumomin Najeriya sun kammala kwashe ƴanƙasar daga Afirka ta Kudu bayan ƙazancewar zanga-zangar ƙyamar baƙi a ƙasar.

    A yau ne jirgi na ƙarshe kuma na shida ɗauke da ƴanƙasar 306 ya sauka a filin jirgin saman Legas.

    Zuwa yanzu fiye da ƴan Najeriya 1,200 ne hukumomin ƙasar suka kwaso a ƙarkashin nwani shirin gwamnatin ƙasar na mayar da ƴanƙasar gida bayan ɓarkewar zanga-zangar ƙyamar baƙi..

    Zanga-zangar wadda a wasu yankunan ake yinta lafiya, ta ƙazance a wasu yankunan har da kisa.

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta nemi diyya daga gwamnatin Afirka ta Kudu ga ƴanƙasarta, waɗanda aka tilasta wa barin sana'o'insu da gidajensu da kuma kadarorinsu a Afirka ta Kudu

  12. Ƴanbindiga sun sace ɗaliban da ke rubuta NECO a jihar Kogi

    Ƴanbindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan jihar Kogi ta tabbatar da yin garkuwa da ɗalibai huɗu da ke rubuta jarrabawar NECO da wasu malamai biyu cikin har da shugaban makarantar.

    Cikin wata sanarwar kakakin rundunar ƴansandan jihar ASP Salisu Oyiza ta fitar ta ce lamarin ya faru ne ranar Talata da yamma lokacin da ɗaliban ke tsaka da rubuta jarrabawar NECO a makarantar Sakandiren Edo-Ekina da ke yankin ƙaramar hukumar Dekina.

    Ƴansan sun kuma ce sun kai ɗaukin gaggawa tare da ƙaddamar da bincike kan lamarin.

    “Tawagar hadin giwar jami'an tsaro sun gaggauta ƙaddamar d aneman ɗaliban, waɗanda har yanzu kuma suna neman jami'an'', in ji sanarwar.

    ASP Oyiza ta ce zuwa yanzu jami'an tsaro sun kuɓutar da ɗalibi ɗaya, yayin da suke ci gaba da neman sauran tare da farautar maharan.

    Lamarin na zuwa kwanaki bayan kuɓutar da ɗaliban makarantar jihar Oyo da suka kwashe makonni a hannun ƴanbindiga.

  13. Iran ta yi barazanar rufe hanyoyin fito na ƙasashen Gulf

    Ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun juyin juya halin Iran sun yi barazanar rufe duka hanyoyin da ƙasashe ƙawayen Amurka ke fitar da kayyakinsu zuwa ƙetare a matsayin martani ga datse tasoshin ruwanta da Amurka ke yi.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar sa'o'i bayan da Amurka ta sanar da datse tasoshin ruwan, ta ce za ta lalata hanyoyin fiton kayayyaki da ƙasashe ƙawayen Amurka ke amfani da su, idan aka ci gaba da toshe wa Iran hanyoyin fitar da manta.

    "Tun da aka datse wa Iran hanyoyin fitar da mai da iskar gas ɗinta domin durƙusar da tattalin arzikinmu, wadda ke zama barazana ga tattalin arzikin ƙawayen Amurka, to muma a jira namu matakin na datse hanyoyin fiton ƙasashen'', in ji sanarwar da IRGC.

  14. An yanke wa sojan Isra'ila hukuncin ɗaurin shekara biyar

    sojan Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojan Isra'ila ta ce ta yanke wa wani sojanta hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari saboda samunsa da laifin aika wa wasu jami'an Iran bidiyon yadda sojojin Isra'ila ke kakkaɓo makaman linzami.

    Sojojin Isra'ilar sun ce sojan ya aika bidiyoyi guda biyu waɗanda ''aka biya shi kuɗin tura su'' a lokacin yaƙin kwana 12 tsakanin ƙasashen biyu.

    Haka kuma rundunar sojin Isra'ila ta ce ta same shi da wasu bidiyoyin d ya naɗa a biranen Isra'ila, waɗanda ya aika su ga jami'an na Iran.

    A lokacin yaƙin, Isra'ila ta hana ɗaukar bidiyon wasu keɓantattun wuraren da yaƙi ya lalata.

  15. Amurka na goyon bayan farfaɗo da bututun man Iraƙi da Siriya

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce tana goyon bayan ƙoƙarin da Iraƙi da Siriya ke yi na farfaɗo da wani bututun ɗanyen mai da ya haɗa ƙasashen biyu.

    Wannan na daga cikin jerin matakai da aka sanar a baya-bayan nan don rage tasirin matakin da Iran ta ɗauka na hana jirage ruwa ratsawa ta mashigin Hormuz.

    Wani jami'i ya ce kamfanonin mai na Amurka za su taka rawa wajen sabunta aikin bututun man fetur na Kirkuk-Baniyas, wanda ya kusan daina aiki gaba ɗaya tun bayan mamayar da Amurka ta yi wa Iraƙi a shekarar 2003.

    Shugaba Trump ya ce Iraki za ta iya taka muhimiyar rawa saboda tana da arzikin man fetur kuma za su kulla yarjejeniyoyi da dama da ita.

    Ana sa ran wannan bututun zai riƙa jigilar ɗanyen man fetur daga filayen man Iraki zuwa gaɓar tekun Bahar Rum da ke Siriya.

  16. Mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe - Iran

    Mashigar Hormuz

    Asalin hoton, ..

    Dakarun juyin juya halin Iran sun ce mashigin Hormuz zai ci gaba da kasancewa a rufe, har sai Amurka ta dakatar hare-haren da take kaiwa ƙasar , kwana guda bayan da sojojin Amurka suka sake toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran.

    Dakarun sun yi gargaɗin cewa za su iya faɗaɗa hare-haren da suke kaiwa zuwa wasu hanyoyin fitar da man fetur zuwa ƙasashen waje.

    Ɓangarorin biyu sun sake musayar hare-hare cikin dare, inda kafafen yaɗa labaran Iran suka ce an kai farmaki kan cibiyoyin Amurka da ke Bahrain da Kuwait da Jordan.

    Sojojin Amurka sun ce sun shafe tsawon sa'a bakwai suna kai wa Iran hari .

    Yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta ke rushewa, Shugaba Trump ya sake yin barazanar kai hare-hare kan tashoshin lantarki da gadoji a Iran idan ba ta koma teburin tattaunawa ba.

  17. Assalama alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a wannan shafi domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta da muhawara kan labaran da muke wallafawa.