Mun kai sabbin hare-hare kan sansanonin Amurka a Kuwait - Sojin Iran
Sashen yaɗa labarai na rundunar juyin juya hali ta Iran ya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa ƙasar ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan sansanonin sojin Amurka uku a ƙasar Kuwait.
Bayanin ya ce sansanonin su ne: Sansanin sojin Ali al-Salem da kuma na Arifjan, wadanda aka yi amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai musu hari a yau.
Sai kuma sansanin Doha, wanda ya ƙunshi rumbun ajiye makamai da kayan aiki na sojojin Amurka.