Wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na ranar Lahadi zai kasance ne tsakanin Argentina, wadda ke riƙe da kofin duniya, da Spain, wadda ke riƙe da kofi Turai. Wato me riƙe da kofin Kudancin Amurka za ta kara da mai riƙe da na Turai.
Saboda wasanni biyu na Argentina sun kai lokacin ƙari, hakan ya sa sun buga ƙarin ƙwallo na awa guda fiye da Spain a wannan gasa.
Da ƙwallo 19, Argentina ce ta fi kowace ƙasa zura ƙwallaye a wannan gasa, musamman saboda ƙwarewarta wajen jefa ƙwallo da zarar ta samu ƴar dama. Haka kuma, ta zura aƙalla ƙwall biyu a kowanne daga cikin wasanninta 13 na baya-bayan nan a Gasar Kofin Duniya, tun bayan shan kashin da ta yi da ci 2-1 a hannun Saudi Arabia a wasan farko shekaru huɗu da suka gabata.
Duk da cewa Argentina ta fi Spain zura ƙwallo da guda shida, haka kuma an fi zuwa wa Argentinar ƙwallo a raga sama da Spain ɗin.
Argentina ta zura ƙwallo ɗaya kacal fiye da Spain daga cikin layin 18, inda ta fi hatsarin jefa ƙwallo daga wajen 18 ɗin, domin ƴanwasanta sun zura ƙwallo biyar daga nesa.
A ɗaya ɓangaren kuma, har yanzu Spain ba ta zura ƙwallo ko ɗaya daga nesa ba a gasar.
Duk da cewa ƴawasan gaba huɗu na Faransa suna da kyau da hatsari, sai dai ƴawasan bayan Spain sun saka su a aljihu suka hana su sakat.
Babban dalilin haka shi ne cewa, duk da yabon da ake yi wa Spain kan ƙwarewarta wajen taka leda cikin hikima, ƴanwasanta na kuma yin aiki tuƙuru. Ko da yake ƴanwasan Argentina sun yi gudu fiye da Spain da mita 13.5 gaba ɗaya saboda ƙarin lokaci, Spain ta fi yin gudun fanfalaki a kowane minti 90 na wasa.
A gefe guda kuma, Argentina ta yi gudu ƙasa da dukkan abokan hamayyarta a wannan gasa, inda bambancin ya kai kilomita 17 gaba ɗaya, amma duk da haka ta yi nasara a kowane wasa.
Salon wasanta da ba ya buƙatar yawan kuzari yana nufin cewa, duk da ƙarin mintuna 60 da ta buga fiye da Spain, ba za ta shiga wasan ƙarshe da giɓin gajiya ba, musamman ma saboda ta hutar da wasu fitattun ƴan wasanta a wasan ƙarshe na rukuni da Jordan.
Spain da Argentina duk sun fi nuna ƙwarewa wajen riƙa ƙwallo a mafi yawan wasanninsu. Sai dai Spain ta riƙe ƙwallo da kashi 51 ne a wasan kusa da na ƙarshe da Faransa, yayin da Argentina ta riƙe ƙwallo da kashi 48 kacal a nasarar da ta samu da ci 3-0 kan Algeria a matakin rukuni. Wannan yana nuna cewa ba lallai ne su fi riƙe ƙwallo ba kafin su yi nasara.
Spain ta fi nuna ƙwarewa wajen ƙwallo a sama, amma Argentina ta ƙara amfani da wannan salon. Daga irin wannan ƙwallo ne Lautaro Martínez ya ci ƙwallon nasara a kan Ingila.
Duk da cewa yawancin ƴanwasan ƙasashen biyu ba su yi zara da yawa ba a gasar, amma duk da haka Messi da Yamal sun ƙoƙarta.
Ƙasashen biyu da za su buga wasan ƙarshe sun yi yunƙurin ratsewa sau 209, inda a ciki Messi da Yamal ke da kashi 43 wato yunƙuri 90.
Matashin ɗanwasan na Spain ne ya fi kowane ɗanwasa yunƙurin zara a gasar, inda ya yi yunƙuri sau 42 daidai da ɗanwasan Brazil, Vinicious Jr.
Hotunan magoya baya gabanin take wasa: