Tottenham na sa rai kan Savinho, Madrid ta ja da baya kan Rodri

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham Hotspur na da kwarin gwiwar kammala cinikin ɗan wasan gefe na Brazil daga Manchester City, Savinho, mai shekara 22. (Fabrizio Romano)
A wani labarin kuma, Real Madrid ba ta da niyyar sayen ɗan wasan tsakiya na Spain daga Manchester City, Rodri, mai shekara 30, a wannan bazara.(Athletic - subscription required)
Kulob din AC Milan na ci gaba da sanya ido kan ɗan wasan tsakiya na Ingila daga Manchester City, Phil Foden, mai shekara 26.(Tuttosport, external).
Sai dai duk wata yiwuwar cinikin Foden za ta dogara ne kan ko AC Milan za ta iya sayar da ɗan wasanta na gaba ɗan Portugal, Rafael Leao, mai shekara 27.(Tuttosport, external).
Mai tsaron baya na Leicester City, Ben Nelson, mai shekara 22, ya shaida wa kulob dinsa cewa yana son barinsa, yayin da Manchester United da West Ham United ke nuna sha'awarsu a kansa.(Mail)
Arsenal na dab da ɗaukar matashin ɗan baya na Ingila Elijah Upson, mai shekara 18, bayan ya ƙi sabunta kwantiraginsa da Tottenham Hotspur.(Fabrizio Romano)
Rahotanni sun ce ɗan wasan tsakiya na Portugal Joao Palhinha, mai shekara 31, zai koma Bayern Munich domin fara shirye-shiryen kakar wasa, inda rahotannin da ke cewa zai koma Aston Villa suka zama ba gaskiya ba.(Sky Germany)
Liverpool na shirin sayen matashin ɗan wasan tsakiya na Colombia mai shekara 17, Samuel Martinez, daga Atletico Nacional kan kuɗin kusan fam dubu 750.(Athletic - subscription required)
Real Madrid da Barcelona da kuma Atletico Madrid duk suna sha'awar mai tsaron bayan Argentina na Tottenham, Cristian Romero, mai shekara 28.(Teamtalk)
Juventus ce ke kan gaba a tseren neman ɗan wasan gaba na Amurka daga Monaco, Folarin Balogun, mai shekara 25, inda take gaban Borussia Dortmund da Sunderland.(Mundo Deportivo)
Chelsea na ci gaba da tattaunawa kan ɗaukar mai tsaron bayan Faransa na Crystal Palace, Maxence Lacroix, mai shekara 26. Sai dai farashin kusan fam miliyan 70 da Palace ke nema na hana samun ci gaba cikin sauri.(Caught Offside)
Har yanzu Juventus na sha'awar ɗan wasan gaba na Brazil daga Tottenham, Richarlison, mai shekara 29.(Gazzetta dello Sport - in Italian)
A ƙarshe, Everton ce ke kan gaba wajen ɗaukar ɗan wasan gefe na Ingila daga Ipswich Town, Jaden Philogene, mai shekara 24.(Football Insider)















