Iran ta nace kan ci gaba da iko da Mashigar Hormuz
Iran ta sake jaddada ƙudurinta na ci gaba da iko da Mashigar Hormuz bayan kammala zagayen farko na tattaunawa da Amurka a ƙasar Switzerland.
Da yake magana da talabijin din gwamnatin Iran yayin dawowarsa daga tattaunawar, babban mai shiga tsakani na ƙasar ya bayyana cewa tafiyar da mashigar ba za ta koma yadda take kafin yaƙin ba.
Ya ce Iran za ta ci gaba da taka rawa wajen sarrafa zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin, tare da tabbatar da cewa an kiyaye buƙatun ƙasar.
Haka kuma, ya bayyana cewa Iran da Amurka sun amince da kafa wasu hanyoyin haɗin gwiwa na wucin gadi na kwana talatin, ciki har da layin waya kai tsaye da cibiyar sadarwa, domin sauƙaka zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar.
A nasa ɓangaren, sakataren kudi na Amurka Scott Bessent ya ce Washington za ta dakatar da takunkumin da ta kakabawa man Iran na tsawon kwanaki sittin, domin bai wa tattaunawar damar ci gaba.