Glasner ya zama kocin Nottingham Forest na biyar cikin shekara guda
Hukumar ƙwallon ƙafar Belgium ta soki hukuncin FIFA kan Balogun
Rahoto kai-tsaye
Ibrahim Yusuf Mohammed da Haruna Ibrahim Kakangi
Yadda Moroko ta kawo wannan matakin
Moroko ta yi rashin sa'a ta tashi canjara a wasanta na farko na rukuni da Brazil amma nan da nan ta samu tsallakawa zuwa zagayen gaba. Yanzu kuma ta kawo wannan matakin sau biyu a jere, ita ce ƙasar Afrika ta farko da ta yi hakan.
Asalin hoton, BBC Sport
Yadda faransa ta kawo wannan matakin
Faransa ta taka rawar gani a gasar bana.
A wasanni biyar, ta zura kwallaye 14 kuma ta zura mata biyu amma a wasan yau zai zama babban jarabawar da ta fuskanta a gasar bana.
Asalin hoton, BBC Sport
Faransa na harin zuwa wasan daf da na ƙarshe sau uku a jere
Asalin hoton, Getty Images
Faransa na neman samun gurbi a matakin kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya a karo na uku a jere, bayan ta cimma hakan a shekarun 2018 (inda ta lashe kofin) da 2022 (inda ta zo ta biyu).
Ƙasashe biyu ne kawai suka taƊa kaiV wa matakin kusa da na Ƙarshe a gasa uku a jere: Jamus (sau huɗu tsakanin 2002 da 2014, da kuma sau uku tsakanin 1982 da 1990) da kuma Brazil (sau uku tsakanin 1994 da 2002).
Bouaddi ya kafa tarihi
Asalin hoton, Getty Images
Ayyoub Bouaddi, ɗan wasan Morocco mai shekaru 18 da kwana 280, shi ne ɗan wasa na biyu mafi ƙanƙancin shekaru da ya taɓa buga wasan daf da na kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya, inda Pele ne kaɗai ya fi shi karancin shekaru wanda ya ke da shekaru 17 da kwana 239 a lokacin da ya fafata a gasar 1958 a wasan da Brazil ta kara da Wales
Al'ummar Moroko na son mu lashe wannan kofin - El Ouahdi
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan bayan Moroko Zakaria El Ouahdi ya na magana kafin wasan: "Muna jin daɗi. Ina jin daɗin buga irin wannan wasan da babbar tawaga irin wannan. Ina tsammanin zai zama babban wasa. Da farko, batu ne na ƙarfafa tunani da ƙwarin gwiwa, wannan shine mafi mahimmanci, sannan bayan haka shine wanda ya fi gudu da kuma wanda ya fi fahimtar dabaru. Mun shirya, ina ganin sun shirya, domin duk mun san cewa nasara za ta ba nu damar shiga wasan kusa da na ƙarshe."
Faransa ba ta yi nasara a ƙarar da ta ɗaukaka kan katin Olise ba
Asalin hoton, Getty Images
Nasarar da Faransa ta samu a kan Paraguay wasa ne da ya ja hankali, amma ba saboda dalilai na ƙwallon ƙafa ba.
Ƴan wasan Paraguay sun zo ne da niyyar artabu, kuma wasan ya kusa zama hakan.
Michael Olise ya karɓi katin gargaɗi sakamakon karo da suka yi da Matias Galarza kuma an yi watsi da ƙarar da Faransa ta ɗaukaka ta na neman a soke katin.
Don haka idan Olise ya samu kati a yau, ba zai buga wasan kusa da na ƙarshe ba – idan Faransa ta samu tsallakawa.
Ƴan wasan Moroko
An yi sauye-sauye biyu a tawagar Moroko inda Anass Salah-Eddine da Chemsdine Talbi za su buga wasa, sakamakon raunin da Ismael Saibari ke fama da shi, sai kuma Redouane Halhal yana cikin ƴan wasan da za su iya shigowa daga benci.
Asalin hoton, BBC Sport
Morocco XI: Bounou, Salah-Eddine, Mazraoui, Diop, Hakimi, El Aynaoui, Bouaddi, El Khannouss, Ounahi, Talbi, Diaz.
Ƴan Benci: Mohamedi, Reda Tagnaouli, Saadane, El Ouahdi, Riad, Belammari, Halhal, Amrabat, El Mourabet, Yassine, Rahimi, Sbai, El Kaabi, Amaimouni.
Ƴan wasan faransa
Didier Deschamps ya yi sauyi ɗaya a jerin ƴan wasa 11 na farko da suka kara da Paraguay, inda Desire Doue ya shigo a madadin Bradley Barcola.
Ƴan Benci: Samba, Risser, Gusto, Konate, T Hernandez, L Hernandez, Lacroix, Tchouameni, Kante, Zaire-Emery, Cherki, Akliouche, Thuram, Barcola, Mateta.
Saibari ba zai buga wa Moroko wasa ba saboda rauni
Asalin hoton, Getty Images
Morocco za ta rasa babban ɗan wasa Ismael Saibari yayin da take neman ɗaukar fansa kan Faransa sakamakon doke ta da ta yi a wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta 2022.
Saibari ya zura kwallo a kowanne wasan rukuni, inda ya zura kwallaye a wasan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Brazil, da nasara 1-0 kan Scotland da kuma nasara 4-2 dkan Haiti.
Ɗan wasan mai shekaru 25, wanda ya tashi daga PSV Eindhoven zuwa Bayern Munich a wannan bazarar, shi ya zura ƙwallon da ta ba shi nasara a kan Netherlands a wasansu na ƙarshe na ƴan 32.
Duk da haka, Saibari ya fuskanci matsala bayan mintuna 22 sakamakon raunin da ya samu a cinyarsa a lokacin da Morocco ta doke Canada da ci 3-0 a wasan ƙarshe na ƴan 16. "Yana fama da rauni amma ina fatan ba ƙarshen gasarsa ba ke nan," in ji kocin Morocco Mohamed Ouahbi.
Moroko za ta nemi ɗaukar fansa kan faransa
Asalin hoton, Getty Images
Wasa tsakanin Faransa da Morocco ba wasan kwata-fainal na gasar cin kofin duniya ba ne kaɗai.
Ga magoya bayan Morocco da dama, ba tu ne na neman ɗaukar fansa.
Shekara huɗu da suka gabata, Faransa ta kawo ƙarshen gasar cin kofin duniya ta ban mamaki da Moroko ta yi a Qatar, inda ta doke ƙasar Afirka da Larabawa ta farko da ta kai wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya.
A yau Alhamis a Boston za su sake haɗuwa, amma a wannan karon Moroko za ta zo ne a matsayin ƙasar da ta cancanci samun gurbi a wasan ƙarshe na gasar.
Tun bayan gasar Qatar, tawagar ƴan ƙasa da shekara 20 ta Morocco ta lashe gasar cin kofin duniya na wannan rukuni, yayin da babbar tawagar ƙasar ta haura zuwa matsayi na shida a jerin ƙasashen duniya na FIFA. Alamun da ke nuna cewa ƙokarin da hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ke yi na bunƙasa ɓangaren wasan matasa na haifar da sakamakon da ake buƙata.
Don haka tambayar da ake yi ba wai kawai ko Moroko za ta iya doke Faransa ba ne.
Tambayar ita ce ko tawagar da ta girgiza duniya a Qatar za ta iya tabbatar da cewa ƙoƙarin da ta yi ba shine kololuwa ba, amma tushe ne da za a ɗaura a kai.
A Qatar, Maroko ta kafa tarihi. A Boston, tana da damar da za ta tabbatar da cewa yanzu ma aka fara.
Ko Moroko za ta iya maimaita irin rawar da ta taka a Qatar?
Asalin hoton, Getty Images
Yayin da nasarar da Moroko ta samu na kaiwa zagayen kusa da na ƙarshe a
Qatar abin mamaki ne, wannan tawagar da ke fafatawa a Amurka ta fi ƙarfin a yi
mata kallon ta ƴan wasa marasa ƙarfi.
A ranar Asabar da ta gabata, zakarun gasar ƙasashen Afirka (wanda
Senegal ke jiran ɗaukaka ƙara bayan wasan ƙarshe mai cike da ce-ce-ku-ce a
watan Janairu), sun sanya ƴan wasa huɗu ne kacal daga cikin waɗanda suka sha
kashi a wasan kusa da na ƙarshe da suka kara da Faransa shekaru huɗu da suka
gabata.
Suna wasa da kuzari da kuma ƙarfin hali, kuma za su zama ƙalubale mafi
tsanani da Faransa ta fuskanta zuwa yanzu a gasar bana.
A ɓangaren ƙasar da ta zo ta biyu a gasar 2022, uku ne kawai daga cikin
ƴan wasan da suka buga wasan kusa da na ƙarshe suka fara wasan da Faransar ta
yi nasara kan Paraguay a ranar Asabar. Fitowar William Saliba, ɗan wasan
tsakiya kuma gwarzon ɗan wasa Michael Olise, suna daga cikin sabbin abubuwan da
Didier Deschamps ya yi tun daga lokacin.
Kylian Mbappe har yanzu shi ne gwarzon ɗan wasa kuma zai ci gaba da
ƙoƙarinsa na doke Lionel Messi na Argentina wajen samun kyautar takalmin zinare
da kuma lambar gwarzon ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a tarihin gasar cin
kofin duniya.
Abin la'akari a nan shi ne rabin
adadin rashin nasarar da Faransa ta yi a gasar cin kofin duniya a cikin wannan
ƙarnin sun zo ne a hannun ƙasashen Afrika (Uku daga cikin shida).
Moroko ba ta yi rashin nasara ba cikin wasanni 34 a jere da ta fafata a
baya ba, amma ba ta taɓa nasara kan Faransa ba wadda ta lashe wasannin bakwai a
jere, yayin da ta yi nasara a wasanni 11 cikin 12 da ta buga.