Amurka da Iran sun sake yi wa juna ruwan wuta a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan ce rana ta biyu da ƙasashen ke ci gaba da kaiwa juna hare-haren makamai masu linzami, duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a watan Afrilu.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce ta samu nasarar kai hare-haren ramuwar gayya domin kare kanta daga Tehran, inda ta farmaki sansanonin sojin Iran da wasu cibiyoyin leƙen asiri a kudancin ƙasar.
Wannan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan Trump ya ce Iran za ta ɗanɗana kuɗarta sakamakon jan ƙafar da take yi wajen tattaunawa kawo ƙarshen yaƙin.
Tehran ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a yankin da ke Bahrain da Kuwait.
Rundunar Juyin Juya Halin Iran ta ce ta harba makamai masu linzamu kan sansanin sojin Amurka da ke Jordan, kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta ruwaito.
Ta kuma ce talalata jiragen yaƙin Amurka masu tarin yawa a harin da ta harba makamai masu linzami 12.
Kafar yaɗa labaran Jordan ta ruwaito cewa ƙasar ta kakkaɓo makamai masu linzami 20.