Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahotanni game da jana’izar Khamenei da wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/07/2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Isiyaku Muhammed, Abdullahi Bello da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Waɗanda suka kamu da cutar Ebola a DR Congo sun haura 1700 tare da kashe aƙalla mutum 600

    Ebola

    Asalin hoton, Amensisa Ifa / BBC

    Yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya karu zuwa dubu daya da dari bakwai da hamsin da tara.

    Ya zuwa yanzu, mutum 600 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar ta yanzu.

    Haka kuma an tabbatar da samun mutum biyu da suka kamu da cutar a wani lardi, lamarin da ke nuna cewa cutar na ci gaba da bazuwa lardin Tshopo da ke yammacin kasar.

    A baya dai cutar ta fi kamari a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

  2. Yau za a yi jana'izar yatollah Ali Khamenei a Hubbaren Imam Reza na birnin Mashhad

    A yau Alhamis ne za a binne gawar Ayatollah Ali Khamenei a makeken Hubbaren Imam Reza na birnin Mashhad, mahaifar marigayin.

    An kwashe kimanin kwana shida ana tarurrukan addu'o'i da kuma bankwana da gawar a biranen Iran da Iraƙi.

    Bayanan bidiyo, Jana'izar yatollah Ali Khamenei a Hubbaren Imam Reza na birnin Mashhad
  3. Sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare a wurare 90 a Iran

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Amurka sun ce sun kammala hare-harensu na baya baya nan a kasar Iran wanda suka kai da jiragen sama , inda suka ce sun kai farmaki a wurare casain, kuma wasu daga cikinsu na kusa da mashigin Hormuz.

    Wakilin BBC ya ce kafar talibijin ta gwamnatin Iran ta ce an kai hari a tsi-birin Abu Musa da ake takadama akai wanda kuma ke kusa da Mashigin hormuz

    An kuma ji karar fashewar abubuwa a yankunan da ke bakin teku ciki harda Bandar Abbas da Cha-ba-har

    Haka kuma an samu katsewar wutar lantarki a wasu yankuna, ciki har da arewacin ƙasar, inda aka lalata wata gadar layin dogo.

    A dayan banagren Iran ta maida martani inda ta ce,dakarunta sun kai hare-hare a sansanonin Amurka da ke wasu ƙasashe makwabta.

  4. Ɓudewa

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,barkanmu da wannan safiya ta ranar Laraba.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai kan jana'izar Ali Khamenei da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.