Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An raba maki tsakanin Ingila da Ghana a karawar rukuni na 12

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Matakin rukuni
Ingila 0 , Ghana 0 a cikakken lokaci
Ingila
Ghana
Full time
Hutun rabin lokaci Ingila 0 , Ghana 0

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. , Ingila 0-0 Ghana

    An buga ta shiga cikin yan wasa daga baya Madueke ya samu damar buga kwallo ya kuma buga amma ta yi sama da yawa.

  2. , Ingila 0-0 Ghana

    Party ya yi wa Kane keta a gaban alkalin wasa, wanda ya busa bugun tazara.

    Wuri mai kyau da Ingila za ta iya amfana.

  3. , Ingila 0-0 Ghana

    Har yanzu Ingila na kai kora, ita dai Ghana so take ta shammaci Ingila.

    Sai dai Gordon ya yi kokarin buga kwallo zuwa gidan Ghana, amma an yi masa keta.

    Alkalin wasa ya busa bugun tazara, an kuma buga Ghana ta fitar da kwallon da ka.

  4. , Ingila 0-0 Ghana

    Karon farko da Ingila ta samu dama, bayan da ta dinga bani in baka daga hagu zuwa dama zuwa tsakiya har ta kai gurin da Kane ya buga, amma cikin ruwan sanyin golan Ghana ya kama kwallon.

  5. , Ingila 0-0 Ghana

    Jude Bellingham ya fadi a cikin gidan Ghana ca yake fenariti ne, amma alkalin wasa ya ce ba komai a ci gaba da wasan. Har yanzu Ingila ba ta samu wata babbar dama ba.

  6. , Ingila 0-0 Ghana

    Ghana ta samu kwana ta buga ta yi waje da yawa, an sake mayar da ita cikin gidan Ingila an ci kasuwar sama da golan Ingila, Jordan Pickford ya fadi kasa, alkaln wasa ya busa ya ce an yi laifi.

  7. , Ingila 0-0 Ghana

    Semenyo ya ja wata kwallo daga gefen hagu yana ta guda da ita zai shiga cikin gidan Ingila, amma Bellingham ya sa kafa ya tare ta shi kuma yana duba wanda zai bai wa kwallon.

  8. An koma zagaye na biyu, Ingila 0-0 Ghana

    An koma zango na biyu, inda za su yi minti 45 da kuma hutun shan ruwa, kafin a tashi daga wannan wasan na bibiyu a cikin rukuni na 12 a gasar cin kofin duniya da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.

  9. Yadda aka gara leda a zangon farko

  10. An je hutu, Ingila 0-0 Ghana

    An je hutun minti 15 daga baya su dawo a karasa zango na biyu minti 45.

    Ingila ce kan gaba a rike kwallo, amma ba ta samu wata dama mai hadari da yawa ba.

    Idan aka tashi haka kowacce tana da maki hurhudu kenan.

  11. An yi karin lokaci, Ingila 0-0 Ghana

    Minti 45 ya cika, kuma an yi karin minti shida daga nan su je hutui, kafin su dawo a karasa fafatawar.

  12. , Ingila 0-0 Ghana

    Ingila ta samu dama mai kyau, inda tun daga baya aka bugo kwallo ta kuma je wajen Bellingham a cikin gidan Ghana ya kuma taba kwallon amma nan da nan mai tsaron baya ya fitar da ita waje, kwana.

  13. , Ingila 0-0 Ghana

    Ghana ta samu kwana, yayin da Semenyo ya yi kokarin shiga bayan Ingila, bai samu dama ba sai ya buga ta taba kafar mai tsaron bayan Ingil ta fita bugun kusurwa.

    Sai dai an buga ba wani hadari.

  14. , Ingila 0-0 Ghana

    An bai wa Declan Rice katin gargadi, sakamakon ketar da yayi.

  15. , Ingila 0-0 Ghana

    Sauran minti biyar lokaci ya cika, na san za a yi karin lokaci da dan yawa.

  16. , England 0-0 Ghana

    Bambanci a bayyane yake.

    Ingila ta raba kwallo sai 283, ita kuwa Ghana tana da 54 - tazarar tana da yawa sosai.

  17. , England 0-0 Ghana

    Ghana ta rufe Harry Kane kamar baya filin, bai samu damar buga kwallon da zai canja lissafin wasan ba.

    Amma dai su kara kula da shi, domin yana samu dama mai kyau shike nan.

  18. , England 0-0 Ghana

    Ghana gabki daya ta koma gida ta bari Ingila na kai mata hare-hare, babu kowa a can gaba koda ta samu kwallo ba wani tasiri da za ta iya yi.

    Ya kamata ta canja wannan salon domin ba zai hana a zura mata kwallo ba.