Trump ya soki matakin majalisar dattawan Amurka kan hana yaƙi da Iran

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kakkausar suka kan matakin da Majalisar Dattawan Amurka ta ɗauka na zartar da ƙudirin dakatar da matakin soja kan Iran.
Trump ya bayyana cewa sanatoci sun aika saƙo ga Iran cewa ba su gamsu da matakan da ya ɗauka kansu ba, yana mai cewa hakan ya “tallafa tare da karfafa gwiwar abokan gaba.”
Majalisar Dattawan Amurka ta amince da ƙudirin da ke buƙatar Trump ya dakatar da duk wani yaƙi da Iran ko kuma ya nemi izinin Majalisar Dokoki kafin ya ci gaba da ɗaukar irin wannan mataki.
Tun da farko ma, Majalisar Wakilai ta Amurka ta amince da irin wannan kudiri.
Sai dai ƙudirin ba ya da cikakken karfin doka, domin ana kallonsa a matsayin na alama ne kawai.














