An sanar da jadawalin jana’izar jagoran addinin Iran, Ayotallah Khamenei

Asalin hoton, Getty Images
Mahukunta a Iran sun sanar da shirin gudanar da jana’izar marigayi jagoran ƙasar, Ayotallah Ali Khamenei, wanda aka kashe a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila a watan Fabrairu.
Rahotanni sun nuna cewa za a fara gudanar da bikin jana’izar ne a babban birnin Tehran daga ranar 4 ga watan Yuli, inda za a yi bukukuwan ban kwana na kwanaki da dama.
Bayan haka kuma, za a ci gaba da jana’izar a birnin Qom, kafin a kammala da binne gawarsa a Mashhad, mahaifarsa, ranar 9 ga watan Yuli.
Hukumar da ke kula da shirye-shiryen jana’izar ta ce ana sa ran dubban jama’a za su halarci waɗannan bukukuwa a fadin ƙasar, sakamakon muhimmancin da marigayin ya ke da shi a siyasar Iran da kuma duniyar Shi’a.
Sai dai rahotannin da ke cewa za a gudanar da jana’izar a Najaf da Karbala ba su samu tabbaci daga manyan kafofin labarai ba, duk da cewa an gudanar da wasu gangamin jana’iza na alama a Najaf a baya.














