Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gasar kofin duniya 2026: Ingila ta fara da cin Croatia 4-2

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Matakin rukuni
Ingila 4 , Croatia 2 a cikakken lokaci
Ingila
Croatia
Full time
Hutun rabin lokaci Ingila 2 , Croatia 2

Muhimman abubuwa

Ingila

  • H. Kane Penalty 12 minutes, Goal 42 minutes
  • J. Bellingham Goal 47 minutes
  • M. Rashford Goal 85 minutes

Croatia

  • M. Baturina Goal 36 minutes
  • P. Musa Goal 45 minutes plus 5
Ba da ƙwallo a ci
Ingila,D. Rice (42 minutes), E. Anderson (47 minutes), B. Saka (85 minutes)
Croatia,P. Sučić (36 minutes), I. Perišić (45 minutes plus 5)

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. , England 3-2 Croatia

    Kwallo ce a daf da ragar Croatia amma taki ta fada raga, inda Rilley ya yi kokarin ci, amma an fitar da ita daga baya aka kara dawo da ita gidan Croatia, amma ta tafi bugun kusurwa.

  2. , England 3-2 Croatia

    Rice ya samu dama ya yi amfani da ita, inda ya buga wata kwallo da karfi da kyar golan Croatia ya ture ta kwana.

    Kuma Rice ya bugun kusurwa babu wani hadari ga Croatia.

  3. , England 3-2 Croatia

    Jude Bellingham ya kusan kara ta uku, amma kwallon ya je bugun kusurwa, kuma Rice ne ya buga ta yi kyau sosai, inda Nico Rilley shi kadai ya sa kai amma kwallon ya fita.

  4. GOAL - Ingila 3-2 Croatia, Jude Bellingham

    Bellingham ya kara na uku, yadda ya samu kwallo daga gefen hagu, haka ya dunga ja har ya shiga gidan Croatia ya kuma buga ta fada raga.

    Lamba 10 tawagar Ingila kenan

  5. An koma zagaye na biyu, Ingila 2-2 Croatia

    Bayan da aka sha ruwa aka koma wasan, za su buga minti 45 daga ciki za su yi hutun shan ruwa kafin a busa tashi.

  6. Yadda aka gara kwallon minti 45

  7. GOAL - Ingila 2-2 Croatia

    Croatia ta farke daf da za a je hutu.

    Za su yi minti 15 daga nan su dawo su karasa minti 45 daga ciki za a yi hutun shan ruwa.

  8. , England 1-1 Croatia

    Modric, mai shekara 40, wanda ke buga gasar cin kofin duniya ta biyar, ya ci gaba da taka rawar gani, shi ne kyaftin din tawagar Croatia, wanda ya ja fenaritin farko da aka zura musu kwallo a raga.

  9. , England 1-1 Croatia

    An yi karin minti biyar, Ingila 2-1 Croatia.

  10. GOAL - England 2-1 Croatia, Harry Kane

    Harry Kane ya ci na biyu, kuma bugun kusurwa aka yi daga wajen Declane Rice zuwa wajen Kane kai tsaye, wanda ya yi tsalle ya saka kai ta fada raga.

  11. GOAL - England 1-1 Croatia, Martin Baturina

    Kwallo ce mai kyau aka ci, sai da aka shiga gidan Ingila aka yanka sai aka bai wa Baturina ita, wanda daga nesa ya buga ta karfi ta fada raga.

    Wasan ya koma 1-1 kawo yanzu.

  12. , England 1-0 Croatia

    Gurin Madueke kamar babu kowa haka yake jan kwallo babu mai tare shi, wannan karon da ya shiga gidan Croatia sai ya dawo da ita, wanda ya kamata ya ci gaba da fuskantar mai tsaron raga.

  13. , Ingila 1-0 Croatia

    Ingila ta samu dama mai kyau, bayan da ta jawo kwallo bani in baka tun daga tsakiya, sai aka buga wav Madueke daga gefen hagu, shi kuwa ya buga cikin gidan Croatia, Jede Bellingham ya yi kokarin taba kwallon amma bai samu ba, sai ya fadi ya kwanta a gaban golan Croatia.

  14. , Ingila 1-0 Croatia

    Har yanzu dai Croatia na kai kora, kamar Ingila tana ganin kwallon nan ta isheta a minti na 30 da muke ciki.

    Ingila ta rage kazar-kazar tun bayan da aka huta aka kuma sha ruwa.

  15. , Ingila 1-0 Croatia

    Tun da aka koma daga hutun shan ruwa, wasan ya koma hannun Croatia sai gara kwallo take hagu da dama amma daga tsakiyar fili, Ingila ta tare gida ba wata matsala.

  16. , Ingila 1-0 Croatia

    An ci gaba da wasan, ko Ingila za ta kara kwallo kafin hutu ko kuma Croatia za ta farke, wadda ta yi ta uku a gasar cin kofin duniya a Qatar a 2022.

  17. , Ingila 1-0 Croatia

    An je hutun shan ruwa, domin yan wasa su huta.

  18. , Ingila 1-0 Croatia

    Jude Belligham ya ja kwallo da gudu zuwa cikin gidan Croatia, amma ya rasa yadda zai yi da ita domin an tare shi ta baci ta koma wajen mai tsaron ragar Croatia.

  19. , England 1-0 Croatia

    Madueke ya samu dama, yana matsawa bayan Croatia, ya buga kwallon amma ta je bugun kusurwa.