Cacar baki ta kaure tsakanin Mbappe da wata ƴar majalisar Paraguay
Ɗan wasan gaba na ƙasar Faransa Kylian Mbappe ya yi alla-wadai da wata ƴar majalisar dattawan ƙasar Paraguay ya kuma bayyana ta a matsayin wadda ba ta cancanci matsayinta ba bayan da ta yi kalaman nuna wariyar launin fata da izgilanci ga asalinsa da kuma iliminsa.
Celeste Amarilla, ƴar jam'iyyar Liberal Radical Party ta Paraguay, ta wallafa kalamn na ta ne a shafinta na dandalin X bayan da ƙasarta ta sha kashi a hannun Faransa a zagaye na yan 16 a gasar cin kofin duniya.
Mbappe ya mayar da martani inda ya ce: “Madame Celeste Amarilla, ke mace ce mara mutunci kuma ba ki cancanci matsayinki ba. "Ba ki wakiltar Paraguay, ƙasar da ta nuna karamci da jajircewa a lokacin wanna gasar.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Faransa (FFF) ta sanar da shirin gurfanar da Amarilla a gaban kotu, inda ta bayyana kalamanta a matsayin abin "kyama".
Gwamnatin Paraguay ta bayyana cewa tana "yin alla-wadai da kuma ƙin amincewa da kalaman" da Amarilla ya yi, inda ta ce sun "saɓa wa ɗabi'u da ƙa'idojin da ke karfafa zaman lafiya da mutunta mutuncin ɗan adam, waɗanda kasarmu ke ingantawa."
Kalaman na Amarilla sun zo ne bayan na tsohon mai tsaron ragar Paraguay, Jose Luis Chilavert, wanda kafin a fara wasan ya ce tawagar ƙasarsa za ta fafata ne da "kungiya daga Afirka".