Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Mbappe zai lashe takalmin zinare a wasan Faransa da Ingila?
Tawagar Faransa za ta kara da ta Ingila a wasan neman matsayi na uku a gasar cin kofin duniya ranar Asabar.
Faransa ta ci karo da cikas a wasan daf da karshe da Sifaniya ta doke ta 2-0, ita kuwa Ingila ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Argentina mai rike da kofin mai uku jimilla.
Wasan nan shi ne na 103 a Gasar Kofin Duniya ta 2026 da zai tance kasar da ta kare a mataki na uku, wadda ta yi nasara da kuma ta huɗu, wadda za a doke.
Wannan ita ce dama ta karshe da Kylian Mbappe ya samu don kara yawan kwallayensa takwas da ya ci iri ɗaya da yawan na Lionel Messi domin lashe ƙyautar takalmin zinare da ake kira Golden Boot, yayin da Harry Kane da Jude Bellingham, wadanda kowannensu ke da ƙwallo shida raga, suma za su iya neman lashe wannan kambu.
Ko Faransa za ta lashe matsayi na uku kuwa?
Da yake ɗan wasan Real Madrid, Kylian Mbappe na kan ganiya, duk lokacin da tawagar Faransa ke buga gasar cin kofin duniya tana yin kokari da nuna bajinta.
A wasan cikin rukuni a bana ta fara da doke Senegal 3-1 da yin nasara 3-0 a kan Iraki, sannan ta lallasa Norwar 4-1 a karawar karshe ta cikin rukuni.
Daga nan Faransa ta kai zagayen na biyu, inda ta caskara Sweden 3-0 da fitar da Paraguay a zagayen ƴan 16 da yin nasara a kan Morocco a kwata fainal.
Tawagar da Didier Deschamps ke jan ragama ta sa ran kaiwa zagaen karshe, amma sai ta ci karo da cikas a hannun Sifaniya, wadda ta doke ta 2-0 ranar Talata a wasan daf da karshe da suka buga a birnin Dallas.
Faransa na shirin buga wasan neman matsayi na uku karo na hudu a tarihin gasar cin kofin duniya, daga ciki ta yi nasara a 1958 a kan Jamus ta Yamma da kuma doke Belgium a 1986, yayin da ta yi rashin nasara a hannun Poland a 1982.
Wace ƙungiya ce za ta huce haushi?
A nata bangaren kuwa, Ingila ta yi wasanni masu ban mamaki da ya kai ta matakin nan da take ciki, koda yake fatan da ta yi shi ne zuwa karawar karshe.
Tawagar Ingila ta fara da yin nasara 4-2 a kan Crotia a wasan farko a cikin rukuni, sannan ta tashi ba ci da Ghana da kuma doke Panama 2-0 a wasan karshe a rukuni na 12.
Ingila ta fuskanci kalubale a hannun Congo DR a zagayen tawaga 32, kafin daga baya Kane ya ci mata ƙwallo biyu da ta zagayen gaba.
Daga nan Ingila ta samu nasarar fitar da Mexico mai masaukin baƙi a zagayen ƴan 16, sannan ta doke Norway a zagayen kwata fainals.
Ingila ta ci karo da koma baya a hannun Argentina abokiyar hamayyarta da ta yi nasara 2-1 a wasan daf da karshe, duk da Ingila ce ta fara cin ƙwallo a zagaye na biyu, sai ta koma tsare gida duk da sauran lokaci da yawa kafin a tashi wasan.
Haka ne ya bai wa Argentina damar farke ƙwallo da kara na biyu, kuma Lionel Messi ne sanadi.
Ingila za ta buga wasan neman mataki na uku a karo na uku, bayan da ta taɓa rashin nasara a hannun Italy a 1990 da kuma Belgium a 2018.
Tarihin Haɗuwar Ingila da Faransa a Gasar Kofin Duniya
Ingila da Faransa sun haɗu sau 32 gabaki ɗayan fafatawa, kuma uku daga cikinsu sun kasance a Gasar Kofin Duniya.
Ingila ta lashe wasan rukuni a 1966 da ci 2-0, sakamakon kwallaye biyu da Roger Hunt ya ci.
Ta sake samun nasara a matakin rukuni a 1982 da ci 3-1, bayan kwallaye biyu daga Bryan Robson da daya daga Paul Mariner.
Haɗuwarsu ta karshe ta kasance a wasan kwata fainal a gasar 2022 a Qatar, inda Faransa ta yi nasara da ci 2-1.
Aurelien Tchouameni da Oliver Giroud ne suka ci kwallayen, inda Kane ya ci ɗaya, wanda ya ɓarar da fenariti.
Ƴan wasan da ake sa ran za a fara karawar da su
Ƴan wasan Faransa 11 da ake sa ran fara wasan da su:
Maignan; Gusto, Lacroix, Konate, T Hernandez; Zaire-Emery, Kante; Olise, Cherki, Doue; Mbappe
Ƴan ƙwallon Ingila 11 da ake sa ran za a fara karawar da su:
Henderson; Chalobah, Guehi, Stones, Spence; Mainoo, Anderson, Rogers; Madueke, Kane, Rashford
Takalmin zinare
Wani da yake jan hankali a game da wasan shi ne batun lashe takalmin zinare, wanda ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe ke nema.
A yanzu dai Messi ne a gaba da ƙwallo 8, sannan ya taimaka aka zura huɗu. Shi ma Mbappe yana da ƙwallo 8, amma ya taimaka ne an zura uku, wanda hakan ya sa Messi ke gaba da shi.
A wasanninsu na ƙarshe za a iya gane wanda zai lashe kyautar, inda Mbappe zai ƙarasa wasan ƙarshe yau, shi kuma Messi ai gobe a wasan ƙarshe.
Akwai kuma Erling Haaland wanda shi ne na uku da ƙwallo 7, sai Harry Kane mai ƙwallo 6 a matsayin na huɗu.
Filin wasa na Miami da za a buga karawar
Filin wasan Miami shi ne gidan ƙungiyar Miami Dolphins da ake yin gasar Formula 1 Miami Grand Prix da ta ƙwallon tennis ta Miami Open da Jami'ar Miami da Orange Blossom Classic da wasannin kwallon kafa na kwalejoji na Orange Bowl, tare da Jazz in the Gardens da sauran masu gabatar da wakoki da bukukuwa.
Filin ya karbi bakuncin wasa takwas a FIFA Club World Cup a 2025, ciki har da wasan bude gasar tsakanin Al Ahly FC da Inter Miami CF.
A Gasar Kofin Duniya ta 2026 kuwa, filin na Miami ya karɓi baƙuncin wasan biyu da Cape Verde ta buga, wadda ta bayar da mamaki duk da cewar karon farko da ta buga gasar kofin duniya.
A filin ne Cape Verde ta buga wasa da Uruguay a karawar rukuni da kuma wasan da Argentina ta yi nasara 3-2 da kan Cape Verde da ƙyar da gumin goshi.
Sauran wasannin rukuni da aka buga a Miami sun hada da tsakanin Saudi Arabia da Uruguay, da na Portugal da Colombia da wasan da Brazil ta doke Scotland da ci 3-0.
Ingila ta riga ta buga wasa a wannan filin, inda tayi nasarar yin waje da Norway da ci 2-1 a zagayen kwata fainal.