An tashi a filin wasan Boston!, Minti 90+7: Faransa 2-0 Moroko
Faransa ta doke Moroko, ta kai wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya sau uku a jere.
Yanzu za ta jira ƙasar da ta yi nasara tsakanin Spain da Belgium.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ibrahim Yusuf Mohammed da Haruna Ibrahim Kakangi
Faransa ta doke Moroko, ta kai wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya sau uku a jere.
Yanzu za ta jira ƙasar da ta yi nasara tsakanin Spain da Belgium.
Jean Phillipe Mateta ya canji Kyllan Mbappe, Bradley Barcola kuma ya shigo a madadin Desire Doue.
Faransa ce kasa ta farko da ‘yan wasanta biyu suka ci kwallo 5 zuwa sama a gasar kofin duniya daya (Dembele 5, Mbappe 8) tun daga shekarar 2002, lokacin da ‘yan wasan Brazil biyu suka yi irin haka (Rivaldo 5, Ronaldo 8).
Dole ne Moroko ta fito ta buga wasa idan har ta na son ta kai labari.
Ousmane Dembele!!! Faransa ta ci ƙwallo biyu cikin minti shida. Moroko ta shiga damuwa.
Mbappe ya jefa ƙwallo a ragar Moroko, duk da cewa bai yi wasa kamar yadda aka saba gani yana yi a gasar bana ba, amma duk da haka ya lallaɓa ya jefa ƙwallonsa na takwas a wannan gasar.
Hari ɗaya kacal Moroko ta kai a wasan ya zuwa yanzu, yayin da Faransa ta ta kai hari 13.
Ko lamarin zai sauya idan aka dawo hutun rabin lokaci?
Har yanzu Moroko ba ta kai wani harin kirki ba a wasan
Desire Doue ya kai hari mai haɗari amma golan Moroko ya tare
Sai da Kylian Mbappe ya jira na minti uku da daƙiƙa 12 kafin ya buga fanaritin. Ko abin da ya sa ya ɓarar ke nan?
Ya buga ta a hankali ta gefen hagun golan Moroko, wanda ya bi ta ya kama.
An bai wa Faransa bugun fenariti
Faransa ta na kutsawa kusa da ragar Moroko cikin sauƙi. Ita ta mamaye wannan wasa tun da aka fara shi.
Moroko ba sa wasa da ɗan wasan gaba mai zura ƙwallo. dabarar ita ce su yi kwantan-bauna su riƙa kai wa Faransa hari.
Desire Doue ya ɗauko kwallon sannan ya miƙa ta ga Kylian Mbappe; ya taɓa sau ɗaya ya kuma buga ta da ƙarfi, amma ta wuce ta gefen raga kaɗan.