Ƙungiyoyin kare muhalli na son Dangote ya dakatar da shirin gina matatar mai a Kenya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar kare muhalli ta Greenpeace Africa ta buƙaci attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya dakatar da shirin gina wata babbar matatar man fetur a yankin gabar tekun Kenya, inda ta ce aikin na iya haifar da mummunar illa ga muhalli.
A farkon watan nan ne aka tabbatar da cewa za a gina matatar, wadda ake sa ran za ta tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a kullum, a tashar jiragen ruwa ta Lamu da ke Kenya, bayan watanni ana ta hasashen ko a Tanzania ne za a gina ta.
"Aikin na barazana ga ɗaya daga cikin muhallin gabar teku mafi muni a Gabashin Afirka, kuma hakan zai jefa yanayin Kenya zuwa mafi muni," in ji mai fafutukar yaƙi da harkokin mai da iskar gas ta Greenpeace Africa, Sherelee Odayar.
Ƙungiyar ta ce matatar da ake sa ran za a ɗauki kusan watanni 30 ana gina ta za ta iya haifar da lalacewar muhalli, gurɓacewar tekuna, kwararar mai da kuma gurbatar iska.
Greenpeace Africa ta buƙaci a dakatar da aikin mai darajar dala biliyan 17, har sai an gudanar da cikakken bincike kan tasirin da zai iya yi ga muhalli da al'umma.
"Bai kamata a amince da fara aikin ba sai bayan an kammala cikakken binciken tasirin muhalli da zamantakewa, tare da bai wa jama'a damar bayyana ra'ayoyinsu da kuma yin cikakken nazari kan illolin tattalin arziki, lafiya da muhalli da aikin zai iya haifarwa," in ji Odayar.



























